Shugaba Buhari zai kai ziyara wani yankin jihar Kaduna ranar Alhamis mai zuwa

Shugaba Buhari zai kai ziyara wani yankin jihar Kaduna ranar Alhamis mai zuwa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Kaduna, inda zai kaddamar da wasu ayyuka a jihar
  • An ce zai kai ziyarar zuwa garin Kafanchan da Zariya, inda zai kaddamar da ayyukan tituna da kasuwa
  • Gwamnatin jihar Kaduna ce ta fitar da sanarwar, inda ta bayyana wasu daga cikin ayyukan da Buhari zai kaddamar

Kaduna - A wani bangare na ziyarar aiki ta kwanaki 2 a jihar Kaduna da zai fara a ranar Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci Kafanchan da ke Kudancin Kaduna da sauran manyan garuruwan jihar domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka.

Buhari zai kai ziyarar kwanaki biyu a jihar Kaduna, wadda za ta fara gobe kuma za ta kare a ranar Juma'a, in ji sanarwa daga gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kada ku kuskura ku zabi yan shaye-shaye matsayin shugabanni, Uwargidar Masari ta gargadi yan Katsina

Buhari zai tafiya Kaduna
Shugaba Buhari zai kai ziyara wani yankin jihar Kaduna ranar Alhamis mai zuwa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar sanarwar:

"Shugaban zai ziyarci manyan garuruwa uku na Kaduna, Zariya da Kafanchan, za kuma a nuna mishi ayyukan tituna a fadin jihar, wanda gwamnatin gwamna Nasir El Rufa'i ta aiwatar."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai ba Gwamna El-Rufai shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya bayyana ayyukan da za a kaddamar da su hade da dandalin Murtala Muhammed da aka gyara, wanda ke tsakiyar garin Kaduna.

Mashawarcin na musamman ya kuma ce har da asibitin cututtuka masu yaduwa, wanda ke Mando, da kamfanin Dangote Peugeot Automobile Nigeria Limited daura da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, da kuma kasuwar Sabon Gari da ke Zariya.

Adekeye ya kuma ce shugaban zai kaddamar da wasu ayyuka kamar gadar sama ta Kawo da aka sake ginawa wadda ke da manyan kusurwowi guda uku da hanyoyin shiga, titin WAFF.

Kara karanta wannan

2023: Yayin da zabe ke gabatowa, gwamnonin PDP za su gana a Fatakwal, jihar Ribas

Shugaban zai kuma kaddamar da ayyukan tituna a Kafanchan da Zariya, kamar yadda Tribune ta tattaro.

Buhari ya dira Maiduguri mintuna bayan harin da Boko Haram ta kai filin jirgi

A wani labarin, shugaba Muhammadu Buhari ya dira Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin ziyarar aiki ta kwana daya mintuna kadan bayan 'yan Boko Haram sun harba roka cikin filin jirgin sama na Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Manyan ma'aikatan gwamnati sun yi wa Buhari rakiya zuwa Borno, jirginsa ya dira a Maiduguri misalin karfe 11.45 na safiyar yau Alhamis.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya na filin jirgin tare da dukkan shugabannin tsaro, da suka isa jihar domin tarbar Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.