Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe ƴan sanda 3 da ƴan sa kai 2

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe ƴan sanda 3 da ƴan sa kai 2

  • Rundunar 'yan sandan jihar Niger ta sanar da kisan 'yan sanda uku da 'yan sa kai biyu da 'yan ta'adda suka yi
  • Rundunar ta sanar da cewa 'yan ta'addan sun yi kwantan bauna ne ga jami'an a Kwanan Dutse da ke karamar hukumar Mariga
  • Sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar ya sanar da cewa jami'ai sun sheke 'yan ta'addan masu yawa a arangamar

Niger - Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta tabbatar da kisan uku daga cikin jami'an ta da ƴan sa kai biyu mazauna yankin yayin da ƴan bindiga su ka yi kwantan ɓauna a Kwanan Dutse, karamar hukumar Mariga da ke jihar.

Kwamishinan ƴan sanda, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da hakan ne a ranar Talata yayin tattaunawar waya da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Minna.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun bindige Basarake a jihar Arewa har lahira a cikin gidansa

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe ƴan sanda 3 da ƴan sa kai 2
Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe ƴan sanda 3 da ƴan sa kai 2. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kuryas ya ce al'amarin ya auku ne a ranar Litinin misalin karfe 4:00 na yamma yayin da Jami'an Tsaron Hadin gwuiwa, wanda ya kunshi ƴan sanda da ƴan sa kai yayin da suka fita sintiri a yankin, Premium Times ta ruwaito hakan.

Ya ce da yawa daga cikin ƴan bindigan "an kashe su yayin arangama da ta dauki sa'o'i".

Musayar wuta tsakanin ƴan bindigan da jami'an tsaron hadin guiwan ya yi sanadin mutuwar ƴan sanda uku da ƴan sa kai biyu na yankin inda wasu suka samu raunuka daban daban,"in ji shi.

Premium Times ta ruwaito cewa, ya bayyana yadda jami'an tsaron hadin gwuiwan a ranar Lahadi suka bankaɗo wani farmakin wata ƙungiyar ƴan bindigan bayan musayar wuta na tsawon awa biyu a kauyen Bari, wurin hanyar Tegina zuwa Kontagora.

Kara karanta wannan

Kebbi: Rayuka 15 ne suka salwanta a farmakin ƴan ta'adda, Jami'ai

A cewar sa, haɗin gwuiwan rundunar ƴan sanda da sojojin an tura su yankin ne su ƙaddamar da farauta "domin damko hatsabibai".

"Muna rokon mazauna yankin da su taimaka wa jami'an tsaron da aka turo da bayanan da zai taimaka wurin damƙar azzaluman.
"Mun fito ne domin mu sheƙe duk mutum ko ƙungiyar mutanen da ta ke kawo cikas ga zaman lafiyar wannan yankin na mu," inji kwamishinan.

'Yan bindiga da ke assasa dokar zaman gida ta IPOB sun balle cocin Katolika a Onitsha

A wani labari na daban, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu son kafa kasar Biafra ne, 'yan awaren IPOB a ranar Talata suka afka wata cocin katolika da ke Onitsha, jihar Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta tattaro bayanai a kan yadda ‘yan bindigan suka afka wa cocin yayin da ake tsaka da bauta sannan suka fara tuhumar faston dalilin sa na tara jama’a yayin da shugaban su, Nnamdi Kanu ya ke hanyar sa ta zuwa kotu.

Kara karanta wannan

Nasara: Gwarazan sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutane

Rahotanni sun nuna yadda aka gurfanar da Kanu gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata da safe. Daily Trust ta ruwaito, masu bautar sun shiga tashin hankali yayin da matasan suka afka cikin cocin da karfi da yaji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng