An gurfanar da Saurayi gaban kotu kan yaƙi ɗaukar nauyin cikin da ya ɗirkawa budurwarsa
- Wani matashin saurayi ya gurfana a gaban kotu a jihar Ogun, bisa tuhumar jefa rayuwar budurwarsa a cikin hatsari
- Masu shigar da ƙara sun shaida wa kotu cewa Yusuf, ya ɗirka wa budurwarsa ciki, kuma ya yi watsi da ita ba tare da ɗaukar ɗawainiyar cikinsa ba
- Kotu ba baiwa Saurayin beli kan N100,000, duk da cewa ya musanta zargin da ake masa
Ogun - Kotun Majirtire ta garƙame matashi ɗan shekara 24, Korode Yusuf, bisa ƙin ɗaukar ɗawainiyar cikin da ya ɗirkawa budurwarsa a jihar Ogun.
Premium Times ta rahoto cewa Yusuf, wanda ke zaune a No. 6 layin Kajola Oluwa, dake yankin Isale Ariya, na fuskantar tuhuma ne kan zargin jefa rayuwar wani cikin hatsari.
Mai gabatar da ƙara, E. O. Adaraloye, ya shaida wa kotu cewa, wanda ake ƙara ya aikata wannan ɗanyen aiki ne a ranar 1 ga watan Maris, 2021, a ɗakinsa da yake zaune.
Adaraloye, ya ƙara da Yusuf ya ƙeƙashe ƙasa, ya ƙi ɗaukar nauyin budurwarsa, wacce ke ɗauke da cikinsa, wanda hakan jefa rayuwarta cikin hatsari ne.
Yace aikata irin haka ya saɓa wa dokar sashi na 339 na kundin manyan laifuka a jihar Ogun, 2006.
Matashin da ake zargin, Mista Yusuf, ya musanta dukkan tuhumar da masu gabatar da ƙara suka ɗora masa.
Wane mataki kotu ta ɗauka?
Alkalin kotun, Mai shari'a A. O. Adeyemi, ta baiwa matashin saurayin beli kan kudi naira dubu N100,000 tare da mutum biyu da zasu tsaya masa.
Alkalin ta kuma kafa sharuɗɗan cewa wajibi ne waɗan da zasu tsaya masa ya kasance suna zaune a yankin da kotu take.
Kuma wajibi ne ya kasance suna aiki kuma su gabatar da takardan shaidar biyan kudin haraji ga gwamnatin jihar Ogun, inji ta.
Daga nan sai mai shari'a ta ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 21 ga watan Janairu, 2022.
A wani labarin na daban kuma Kotu ta yanke wa wani tsohon Sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya
Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yanke wa korarren tsohon sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya bisa aikata babban laifi.
Alkalin kotun ya bayyana cewa kotu ta samu mutum biyun da laifin aikata fashi da makami kan wani mai gidan man fetur.
Asali: Legit.ng