Abin da yasa Gwamnatin Tarayya ba za ta dena karɓo rancen kuɗi ba, Lawan

Abin da yasa Gwamnatin Tarayya ba za ta dena karɓo rancen kuɗi ba, Lawan

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce har sai hukumomin da suke samar da kudaden shiga sun yi abubuwan da suka dace kafin gwamnatin tarayya ta daina rancen kudaden daga kasashen ketare
  • Lawan ya yi wannan furucin ne a ranar Talata yayin jawabin yi wa sanatoci maraba da dawowa daga hutun kirsimeti da na sabuwar shekara
  • A cewarsa akwai bukatar samar da kudaden shiga masu yawa don gwamnati ta yi amfani da su wurin yin ayyukan ci gaban kasa

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce Gwamnatin Tarayya za ta cigaba da rancen kudi matsawar hukumomin da ke samar da kudaden shiga ba su dinga yin kokari yadda ya dace ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanatocin jihar Katsina 2 sun yi watanni 25 a Abuja, ba su kawo korafi ko shawara 1 ba

Lawan ya yi wannan tsokacin ne a ranar Talata yayin jawabi ga ‘yan majalisar yayin yi musu maraba daga dawowa hutun kirsimeti da sabuwar shekara.

Abin da yasa Gwamnatin Tarayya ba za ta dena karɓo rancen kuɗi ba, Lawan
Lawan: Dalilin da yasa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ba za ta dena karbo rancen kudi ba. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewarsa akwai bukatar samar da kudaden shiga masu yawa don gwamnati ta dinga amfani da su tana yi wa kasa ayyukan da suka dace.

Lawan ya ce majalisar za ta yi aiki da hukumomin don cin ma makasudin

Daily Trust ta bayyana yadda ya ce majalisar ba za ta yi sanya ba har sai ta tabbatar an samar da mafita ta hanyar amfani da hukumomi masu samar da kudaden shiga wurin hana gwamnatin yin rance.

Kamar yadda Lawan ya ce:

“Duk aro kudade aka yi don tabbatar da kasafin shekarar 2022. Kasar mu tana tsaka mai wuya. Wajibi ne mu samar da ababen more rayuwa a bangarori daban-daban na kasar nan don samar da ci gaba.

Kara karanta wannan

Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni

“Sai dai ba ma samar da kudade masu yawa da hukumomin da ake amsar haraji. Har sai an fara kafin kasar nan ta daina rancen kudi don yin ayyukan ci gaba.

Akwai bukatar bunkasa tattalin arzikin kasa

Ya ci gaba da cewa:

“Za a ci gaba da aron kudi babu kakkautawa don yin ayyuka. Ya kamata mu yi gyara akan tattalin arziki (GDP). Da kusan kaso 8% na haraji na kason GDP, yanzu haka kasar mu tana samun 50% na abinda take bukata na haraji ga GDP na 15% don tallafa wa tattalin arzikin kasa.
“Majalisar dattawa za ta taimaka wurin hada kai da hukumomin da ke amsar haraji don burin kasa ya cika a shekarar 2022 a samu kudin haraji mai yawa. Hakan zai taimaka mana wurin rage yawan bashin da kasa take ci wanda ya ke mayar da mu baya.”

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164