Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari ta sake zayyano manyan laifuka kan Nnamdi Kanu
- Gwamnatin Najeriya ta sake shigar da sabbin kararraki kan Nnamdi Kanu, wanda za a fara saurara nan ba da dadewa ba
- Gwamnatin a baya ta kamo Kanu a waje, sannan ta zarge shi da laifukan cin amanar kasa da dai sauransu
- Yanzu haka, Kanu zai fuskanci tume-tuhume sama da 15 da gwamnatin Buhari ta yiwa kwaskwarima
Abuja - A ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta shigar da sabbin tuhume-tuhume na ta’addanci a kan tsararren shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB; Nnamdi Kanu.
FG, a tsarin gyaran tuhumar da ta shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta kara yawan tuhume-tuhumen kan na farko da ta ke yiwa Nnamdi Kanu, Vanguard ta rahoto.
Shugaban kungiyar ta IPOB a baya yana fuskantar tuhume-tuhume bakwai na cin amanar kasa.
A halin yanzu kuwa, zai fuskanci sabbin tuhume-tuhume 15 da aka yi wa kwaskwarima mai lamba FHC/ABJ/CR/383/2015 da Daraktan shigar da kara na DPP, MB Abubakar ya sanya wa hannu.
FG ta gyara tuhumen-tuhumen ne sa’o’i 24 kacal kafin lokacin da aka shirya fara sauraron karar Kanu a gaban mai shari’a Binta Nyako, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A ranar 2 ga watan Disamba ne dai kotun ta sanya ranar Talata domin sauraren wasu kararraki da ke gaban kotun, ciki har da wanda Kanu ya shigar na a sallame shi da kuma wanke shi.
Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu
A wani labarin, The Cable ta ruwaito cewa, an sake gurfanar da Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara (IPOB) a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin ta’addanci.
Kwanan nan gwamnatin tarayya ta sake shigar da laifukan da ake tuhumarsa da shi guda bakwai kari a kan laifuka biyar da a baya yake amsa su, wadanda suka hada da aikata cin amanar kasa da ta’addanci.
An fara zaman kotun a ranar Alhamis da karfe 10 na safe. Lokacin da aka karanta masa laifukan, shugaban IPOB din ya musanta aikata laifin.
Asali: Legit.ng