Ta'adin yan bindiga: Abinda gwamna Masari ya gaya wa Bola Tinubu yayin da yakai masa Ziyara Katsina
- Gwamna Aminu Bello Masari, ya yi magana kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka don kawo karshen matsalar tsaro yayin ziyarar Tinubu
- Masari yace gwamnatinsa ta fito da wani sabon tsarin tsaro da ya ƙunshi sarakuna, shugabannin addinai da sauran su a kowane ƙauye
- Yace gwamnatin Katsina ba ta tsaya nan ba, ta fara aikin kafa cibiyoyin warware matsaloli tsakanin mutane ba tare da zuwa kotu ba
Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace gwamnatinsa ta kafa tsarin tsaron ƙauyuka a yaƙin da take domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar, musamman yan bindiga.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin jagoran APC na ƙasa, wanda ya kai ziyarar ta'aziyyar kashe Kwamishina, Rabe Nasir, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
A cewar gwamnan, sabon tsarin da gwamnatinsa ta kafa a ƙauyuka ya ƙunshi sarakunan gargajiya na yankuna, shugaban manyan addinai biyu da suka fi ƙarfi, da kuma shugabannin mahauta.
Yace mambobin wannan tsari sun haɗa da shugabannin masu Aski, yan uniyon dake aiki a tashar Mota, jagororin ƙungiyoyin sa'kai, da duk masu taka rawa wajen cigaban al'unma.
Masari yace:
"Duk waɗan nan mun saka su a sabon tsarin tsaron da muka kafa, wanda ya kunshi kowane ɓangare na al'umma. Mun saka sarakunan gargajiya a ciki, saboda lamari ne da ya shafi al'ummar su."
"Bayan haka mun kafa cibiyar warware rikici wanda za su yi aiki ƙarƙashin Ofishin babban alƙali na jiha, kuma yanzu haka muna kan aikin kara wasu cibiyoyin samar da maslaha 40 a faɗin jihar mu, tuni suka fara aiki."
"Abin da zai baku mamaki shine guda 8 daga cikin waɗan da muka kafa, sun warware matsaloli fiye da waɗan da kotunan mu ya dace su yi."
Wane aiki waɗan nan cibiyoyi zasu maida hankali?
Gwamna Masari ya ƙara da cewa waɗan nan cibiyoyi za su yi kokarin magance rikicin mai gida da yan haya da kuma rikicin da ya shafi mallakar filaye.
"Kananan matsaloli kamar na magudanar ruwa, kamar Dabbar makoci ta shiga gidan wani ta yi barna, da rikici tsakanin iyalai. Waɗan nan wasu abubuwa ne da ba sai an je kotu ba."
"Zaiyi wahala kuje kotu kuma ku fito cikin farin ciki kuma abokantaka ta cigaba, amma idan cibiya ce irin wannan za'a sasanta komai ba tare da karya wata alaƙa ba."
A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai wani mummunan hari Jihar Kebbi, sun ƙona dandazon mutane
Mutane da dama sun mutu yayin wani mummunan hari da yan bindiga suka kai ƙauyen Ɗan Kade, dake yankin Unashi, ƙaramar hukumar Zuru a jihar Kebbi.
Wasu tsagerun yan ta'adda masu ɗimbin yawa ne suka mamaye kauyen da tsakiyar daren ranar Lahadi, inda suka hallaka dandazon mutane.
Asali: Legit.ng