Da Duminsa: Fusatattun fasinjoji sun afka ofishin kamfanin jirgin Azman da ke Kano akan soke tashin jirgi
- Fusatattun fasinjoji sun afka ofishin kamfanin jirgin sama na Azman da ke Kano ranar Litinin saboda sun soke tashin jirgin karfe 7 na safe da zai je Legas
- An samu bayanai akan yadda jami’an kamfanin jirgin Azman suka tura wa fasinjoji sako ta yanar gizo akan fasa tashin ana saura mintuna kadan lokaci yayi
- Wasu daga cikin fasinjojin sun koka akan yadda aka rusa musu shirin su don wasu kasashen waje za su wuce daga Legas don saboda uzurorin su
Jihar Kano - Fusatattun fasinjojin jirgin sama na Azman sun tayar da kura a ofishin kamfanin jirgin a ranar Litinin bisa fasa tashin jirgin karfe 7 na safe zuwa Legas, Daily Trust ta ruwaito.
An samu bayanai akan yadda kamfanin jirgin ya sanar da fasinjojin batun fasa tafiyar ta sakon yanar gizo ana saura mintuna kadan da lokacin tashin jirgin ya yi.
Wasu fasinjoji sun koka akan uzurorinsu na lafiya don shirin zarcewa kasar waje
Wasu daga cikin fasinjojin, wadanda suka ce suna shirin fita kasashen ketare daga Legas, sun fusata akan yadda ba a sanar da su batun fasa tashin ba sai a kurarren lokaci.
Wasu sun ce za su wuce Legas ne wanda daga can zasu zarce birnin London, Egyt, Dubai, Ghana da sauran kasashe saboda neman lafiya.
Daga baya fasinjojin suka jeru a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) sannan suka afka ofishin kamfanin jirgin da ke titin Zaria don zanga-zanga.
Har yanzu babu kwakkwaran dalilin soke tafiyar daga kamfanin
Har karfe 9:20 na safe lokacin da wakilin Daily Trust yake rubuta wannan rahoton suna ci gaba da zanga-zangar kuma kamfanin jirgin bai sanar da kwakkwaran dalilinta na fasa tashin ba.
Amma Lawal Suleiman, Manajan jirgin saman Azman na jihar Kano, ya tabbatar wa da fasinjojin cewa ana ta shirin mayar musu kudadensu ko kuma a shirya tashin wani jirgin a ranar Laraba da yamma.
Daily Trust ta ruwaito yadda kamfanin jirgin ya taba samun irin wannan matsalar a shekarar da ta gabata wanda ya janyo rikici tsakanin fasinjojin da ma’aikatan a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano bayan rusa wasu tafiye-tafiye da suka yi.
Hakan yasa gwamnati ta kwace lasisin kamfanin jirgin amma daga bisani aka mayar musu.
Miji da mata da suka shiga aikin dan sanda a rana daya, sun zama kwamishinoni a rana daya
A wani labarin, kun ji cewa babban Sufeta na Yan sandan Najeriya, Usman Baba, a ranar Juma'a, ya saka wa Kehinde Longe da matarsa, Yetunde Longe anini a matsayin kwamishinonin 'yan sanda, The Nation ta ruwaito.
Ma'auratan suna daga cikin wadanda Hukumar Kula da Harkokin Yan sanda ta yi wa karin girma tare da wasu 15 zuwa kwamishinoni.
Da ya ke karanto bayani dangane da su, Mai magana da yawun yan sanda, CP Frank Mba ya ce matar da mijin ajin su daya kuma sun shiga aikin dan sandan ne a rana daya a Maris din 1990.
Asali: Legit.ng