Kaduna: Jama'a suna gudun hijira bayan kutsen 'yan ta'adda a kauyen Damari
- Jama'a masu tarin yawa sun tattara komatsansu inda suke tserewa daga yankin damari da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna
- Miyagun 'yan bindiga sun kutsa yankin inda suke ta ruwan wuta, ana zargin farmakin daukar fansa suka je yi saboda gagararren dan bindiga Malam Abba na kula da yankin
- Har ila yau, a ranar Juma'a, an yi mummunar arangama da ta yi ajalin 'yan bindiga da yawa tsakanin wata kungiya da ta Malam Abba, tabbataccen dan Boko Haram
Kaduna - Daruruwan jama'a mazauna yankin Damari da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna suna gudun hijira bayan 'yan ta'adda a babura sun kutsa yankunan su a safiyar Lahadi.
Mazauna kauyen sun sanar da Daily Trust cewa, 'yan bindigan sun bibiyi mambobin kungiyar dan bindiga Malam Abba ne, wanda rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a 2020 suka tabbatar da cewa dan Boko Haram ne.
Ibrahim Hassan, wani mazaunin Damari, wanda ya bar yankin, ya sanar da Daily Trust cewa 'yan bindiga sun tsinkayi yankin wurin karfe goma na safiyar Lahadi, inda ya kara da cewa sun fara gudun ne bayan jin harbin bindiga.
Daily Trust ta tattaro cewa, an yi mummunan arangama a ranar Juma'a tsakanin 'yan bindiga da mukarraban Malam Abba wanda aka kashe 'yan bindiga masu yawa.
Wata majiya daga yankin ta ce, an yi zargin cewa 'yan bindigan sun kai farmaki Damari ne domin daukar fansa saboda ta na karkashin kulawar Malam Abba.
A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce ya tuntubi jami'in da ke kula da yankin da ya hada kai da sauran jami'an tsaro domin ceton jama'a.
Al'amuran 'yan bindiga suna cigaba da kamari a jihar Kaduna duk da tsananta ayyukan sojoji a jihar da sauran jihohin arewa wadanda ake murkushe 'yan ta'adda.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji
A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane sun sace tsohon kakakin majalisar jihar Imo, Lawman Duruji, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Wakilin Punch ya tattaro bayanai akan yadda aka sace Duruji a karamar hukumar Ehime Mbano ranar Asabar a Oriagu yayin da ya ke dawowa daga wani taro.
Sun kuma yi garkuwa da wani dan kasuwa a Owerri, wanda aka fi sani da Ezzybee. A ranar Lahadi aka sace Ezzybee a hanyarsa ta zuwa wurin kallon kwallo.
Asali: Legit.ng