Ta’addanci: Masu kai wa 'yan bindiga bayanai sune babbar matsalar mu, El Rufai

Ta’addanci: Masu kai wa 'yan bindiga bayanai sune babbar matsalar mu, El Rufai

  • Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce masu ba ‘yan bindiga bayanan sirri sune manyan matsalolin da suke kawo cikas wurin yaki da ta’addanci a jiharsa
  • Ya yi wannan furucin ne yayin jawabi a ranar bikin tuna ‘yan mazan jiya a jihar Kaduna ranar Asabar inda yace jami’an tsaro suna iyakar kokarinsu
  • A cewarsa ya kamata shugabannin addini da na anguwanni su mike tsaye wurin sa ido akan shige da ficen mutane don gano bara-gurbi

Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce babbar matsalar da ke cinma jihar tuwo a kwarya da kawo cikas wurin yaki da ta’addanci shi ne masu kai wa ‘yan bindiga bayanai, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan bayanin ne a ranar tuna ‘yan mazan jiya a jihar Kaduna, ranar Asabar inda yace masu kai wa ‘yan bindiga bayanai suna rayuwa a cikin jama’a.

Kara karanta wannan

Rudani: 'Yan Boko Haram sun sace malaman makarantar 'yan sanda a Borno

Ta’addanci: Masu kai wa 'yan bindiga bayanai sune babbar matsalar mu, El Rufai
Ta'addanci: Masu kai wa 'yan bindiga bayanan sirri ne babbar matsalar mu, El-Rufai
Asali: Facebook

Ya ce sojoji da ‘yan sanda suna iyakar kokarinsu

Kamar yadda yayi jawabin:

“Babbar matsalar da ta addabi kasar nan musamman Jihar Kaduna shi ne rashin tsaro kuma sojoji da ‘yan sanda suna iyakar kokarinmu amma ya kamata masu ruwa da tsaki su bayar da tasu gudunmawar.
“Muna rayuwa cikin masu kai wa ‘yan bindiga bayanai. Don haka ya kamata shugabannin addini da na al’umma su dage wurin sa ido akan duk wanda aka ga yana kashe kudi ba tare da sanin hanyar da yake samu ba.
“Akwai yiwuwar mai kai wa ‘yan bindiga bayanai ne a cikin al’umma don haka jama’a su sanya ido kuma suyi gaggawar kai wa jami’an tsaro rahoto.”

A cewarsa gwamnati za ta bai wa mutum kariya idan ya kai rahoton

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki gari a Katsina, sun sanya harajin N10,000 kan kowa

Daily Trust ta bayyana yadda gwamnan ya ce za a bai wa jama’a tabbacin kulawa da lafiyarsu matsawar suka kai bayanan kuma za a yi gaggawar daukar mataki.

El-Rufai ya mika godiyarsa ga sojoji da ‘yan sanda inda yace anata asarar jami’an tsaro sakamakon yaki da ta’addanci kuma ya basu tabbacin cewa gwamnati tana tare da su ta hanyar tallafa musu da dukiya da addu’o’i.

Neja: Ƴan bindiga sun ɗaure ni, ina kallo suka kashe ƴaƴa na 6 ɗaya bayan ɗaya, Dattijo mai shekaru 75

A wani labarin, kun ji cewa a ranar Talata ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Nakuna da Wurukuchi da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar wacce suka janyo asarar rayuka da dama, The Nation ta ruwaito.

Babban tashin hankalin ya ritsa da wani Mallam Yahaya Mota Nakuna mai shekaru 75 wanda a gaban idonsa suka halaka yaransa daya bayan daya.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun yi kaca-kaca da kasuwar 'yan Boko Haram/ISWAP

Yayin da Yahaya ya ke tattaunawa da wakilin The Nation, ya ce sun bar gida zuwa gona a ranar Talata ba tare da sanin babban tashin hankalin da zai same su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

iiq_pixel