Sarki a Arewa ya sha da ƙyar hannun matasa da suka kai hari fadarsa don ya gaza kare su daga harin ƴan bindiga
- Wasu matasa da ake zargin yan kabilar Irigwe ne sun kai hari fadar Sarkin Irigwe, Ronku Aka, a ranar Juma'a inda suka tafka barna
- Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin matasan sun kai harin kan abin da suka kira rashin iya kare su daga hare-haren yan bindiga da sarkin ya gaza
- Rundunar sojojin Najeriya na Operation Safe Haven da ke Plateau ta tabbatar da lamarin ta kuma ce ta tura dakarunta don dawo da zaman lafiya
Jihar Plateau - Wani basarake a Jihar Plateau, Mai martaba, Bra Ngwe Irigwe, Rt Rabaran Ronku Aka, a ranar Juma'a, ya sha da kyar yayin da fusatattun matasa a garinsa suka kai masa hari.
Fusatattun matasan sun lalata fadarsa da ke unguwar Miango, a karamar hukumar Bassa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Aku, wanda ya kai shekaru 80, shine babban sarkin yan kabilar Irigwe a karamar hukumar Bassa inda ake zargin yan bindiga sun kahse mutane da dama sun kuma lalata musu kayayaki a harin baya-bayan nan inda aka kashe mutum 18 a garin Ancha.
The Punch ta ruwaito cewa an gano matasan sun fusata ne kan abin da suka kira gazawar sarkin na kare su daga hare-haren da ake cigaba da kai musu.
Shugaban kungiyar matasan Irigwe ta magantu kan harin
Shugaban kungiyar matasa na cigaban Irigwe, Ezekiel Bini, ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin a Jos, a ranar Juma'a.
Ya ce:
"Yanzu aka sanar da ni cewa wasu mutane da suka kira kansu matasa sun kai hari a fadar babban sarkin mu sun lalata kayayaki. Ban san daga inda matasan suka fito ba amma dai sarkin mu yana nan lafiya.
"Da na tambaya menene matsalar, sun fada min matasan sun fusata ne domin wai sarkin mu baya yin abin da ya dace don hana kashe-kashe, wanda ba gaskiya bane. Ban san abin da suke so ya yi ba domin ya dade yana kokawa cewa wasu da ake zargin yan bindiga ne suka saka masarautarsa a gaba.
"Sau da yawa ya janyo hankalin gwamnati kan matsalar a masarautarsa yana tsamanin gwamnatin wacce hakkin kare rayyuka da walwala mutane ke kanta zata dauki mataki, amma har yanzu matakin da aka dauka bai gamsar ba yayin da ana cigaba da kashe mutane."
Sojoji sun tabbatar da harin
Rundunar sojoji ta Operation Safe Haven, da ke aikin samar da zaman lafiya a yankin ita ma ta tabbatar da kai hari fadar sarkin a ranar Juma'a.
A cewar sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin sojoi, Manjo ishaku Takwa, ta ce:
"An sanar da dakarun Operation Safe Haven hari a fadar Mbra Ngwe Irigwe babban sarkin Irigwe a karamar hukumar Bassa a Jihar Plateau.
"Wasu matasa da ake zargin yan Irigwe na karamar hukumar Bassa ne suka kai harin.
"An tura jami'an Operation Safe Haven su tabbatar dawo da zaman lafiya da doka da odo."
'Yan bindiga sun dira a Kano, sun sace mahaifiyar ɗan majalisa
A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Laraba sun sace mahaifiyar Isyaku Ali-Danja, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gezawa a majalisar jihar Kano.
Daily Nigerian ta rahoto cewa yan bindigan sun afka gidan mahaifiyar dan majalisar ne da ke Gezawa misalin karfe 1 na dare, suka balle kofa sannan suka yi awon gaba da ita.
Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Mr Ali-Danja, wanda ya taba rike mukamin kakakin majalisa, ya ce da farko yan bindigan sun umurci mahaifiyarsa ta bude kofa amma ta ki.
Asali: Legit.ng