FG ta bayyana sharudda 5 da ta gindaya wa Twitter kafin dage dokar haramci
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage dokar dakatar da Twitter a Najeriya. Dage dokar, kamar yadda takardar da Kashifu Inuwa Abdullahi, darakta janar na NITDA yasa hannu, za ta fara aiki ne a tsakar daren 13 ga Janairun 2022.
A watan Yunin shekarar da ta gabata, gwamnati ta sanar da dakatar da Twitter a Najeriya bayan kafar sada zumuntar ta goge wallafar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya ke barazanar magance 'yan awaren IPOB a yaren da suke ganewa.
Wata uku da suka gabata, shugaban kasan ya bayar da umarnin dage Twitter, matukar sun cika sharuddan da aka sanya musu, TheCable ta ruwaito.
Wasu daga cikin sharuddan sun hada da yin rijista aiki a shari'ance, biyan haraji da kuma kiyaye dokokin haramta wallafa kamar yadda dokokin Najeriya suka tanadar.
TheCable ta ruwaito cewa, a yayin sanar da dage haramcin, gwamnatin ta ce Twitter ta amince da kiyaye dukkan sharuddan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rijistar Twitter da CAC
Daya daga cikin sharuddan da gwamnatin tarayya ta bai wa gagarumin kamfanin shi ne rijista da CAC a Najeriya.
Takardar ta kara da cewa, Twitter ta amince za ta yi rijista da CAC.
"Twitter ta shirya bin dokar Najeriya a wata ukun farko na 2022. Za su yi rijista da CAC," takardar tace.
Nada wakilin Twitter a Najeriya
Gwamnatin ta kara da cewa, Twitter za ta nada wakilin ta domin wakiltar ta a Najeriya tare da zama wakilin ta a wurin hukumomin Najeriya.
Twitter za ta biya haraji
Takardar ta kara da shaida cewa, kamfanin Twitter ya amince kan cewa zai dinga biyan haraji a Najeriya karkashin dokokin Najeriya.
Daukan jami'an Najeriya aiki wurin kula da haramtattun wallafa
Gwamnatin tarayya ta ce kamfanin ya amince da cewa zai dauka 'yan Najeriya aiki domin taimakawa wurin tabbatar da bin doka.
Kamar yadda takardar tace, mashigin zai samar da hanya kai tsaye ga jami'an gwamnati da ma'aikatan Twitter na yadda za su kiyaye haramtattun wallafa da suka saba wa dokokin Twitter.
Biyayya ga dokokin Najeriya da al'adunta
Gwamnati ta ce Twitter ta amince za ta mutunta dokokin Najeriya, al'adun kasar da kuma tarihin ta wanda a kan su ne aka gina dokoki.
Kamfanonin Sadarwa sun budewa yan Najeriya Tuwita bayan umurnin Buhari
Yan Najeriya da dama a ranar Alhamis sun bayyana cewa lallai sun samu shiga shafin Tuwita ba tare da amfani da VPN ba bayan Gwamnati ta dage takunkumin da ta sanya tun bara.
Hakazalika Legit.ng Hausa ta gwada shiga Tuwita ba tare da VPN ba kuma ya bude.
Gwamnatin tarayya ta dage dakatar da ayyukan kafar sadarwar Twitter a Najeriya bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, The Cable ta rahoto.
Asali: Legit.ng