Zulum: Mayakan ISWAP sun fi na Boko Haram makamai, dole ne a dakile su
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce mayakan ISWAP sun fi na Boko Haram makamai, hakan ya bijiro bukatar dakile su
- Gwamnan ya karba bakuncin kwamitin kula da harkokin sojoji na majalisar dattawa wadanda suka je masa godiya kan goyon bayan da ya ke bai wa sojoji
- Gwamnan ya jinjina wa gwamnatin shugaba Buhari inda yace tsaro ya inganta tunda 'yan jihar sun koma nomansu da kiwo a yankunansu
Maiduguri, Borno - Farfesa Umara Babagana Zulum, Gwamnan jihar Borno ya ce mayakan ta'addanci ISWAP sun fi na Boko Haram miyagun makamai, don haka dole a dakile su da gaggawa.
Gwamnan ya yi jawabin ne yayin da ya tarbi mambobin kwamitin majalisar dattawa na kula da harkokin sojoji karkashin jagorancin Ali Ndume. Shugabannin sun ziyarci Zulum a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, TheCable ta ruwaito.
Yayin jinjina ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro na tarin nasarorin da suka samu a Borno, Zulum ya bayyana tsananin damuwarsa da karuwar yawan mayakan ISWAP a sassan jihar, musamman a kudancin Borno.
"Zaman lafiya ya fara dawowa a jihar Borno a sannu-sannu. Duk da hakan ba abu mai yuwuwa bane ba tare da agajin gwamnatin tarayya ba," a cewarsa.
Ya kara da cewa:
"Shugabannin rundunonin tsaro suna bamu hadin kai yadda ya dace. Tabbas, kwamandan runduna na yanzu da GOCs suna bamu hadin kai.
"Hakikanin gaskiya, ya kamata muy i wani abu akan ayyukan mayakan ISWAP a jihar Borno. Idan ba a yi wani abu ba dan ganin an wartakesu daga jihar, akwai yuwuwar ba mutanen arewa maso gabas kawai ba, gaba daya kasar zamu dandana kudarmu.
"Mayakan ISWAP suka fi cancantar a ragargaza, sunf i mallakar kayan aiki, sun fi wayau kuma sun fi gogewa fiye da'yan Boko Haram kuma a kullum kara yawa suke. Saboda haka, yanzu ne yakamata a wartakesu."
Gwamnan ya kara da cewa, jihar ta tsayu da kafafunta, musamman a bangaren noma da kiwo a dalilin aje makaman da 'yan ta'adda suka yi kwanan nan, TheCable ta ruwaito.
Acewarsa, tun lokacin da 'yan ta'adda suka aje makamansu, harkar noma ta ninku sau bakwai.
Ya kara da cewa, kafin zaman lafiya ya tabbata a yankin, ya na bukatar yakin sojoji gami da dabarbarun siyasa dan ganin an tarwatsa kuma an tunbuko miyagun don kwatar 'yanci.
A tsokacin da yayi, Ndume ya ce sun ziyarci Borno ne don jinjinawa Zulum game da karfafa sojoji da yake don dawo da zaman lafiya.
"Mun zo dubiya ne, gami da mika godiyar mu ga yallabai akan karfafa sojoji da ka ke, wanda su kansu sun yaba," a cewar Ndume.
Sunaye: Rundunar sojin kasa ta yi girgiza, an sauya wa GOCs da manyan hafsoshi wurin aiki
A wani labari na daban, shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya amince da nadi tare da sauya wa manyan sojojin kasa wuraren aiki duk don ba su kaimin yaki da ta’addanci a kasar nan.
A wata takarda wacce darektan hulda da jama’an soji, birgediya janar Onyema Nwachukwu ya saki a Abuja, ya ce wadanda lamarin ya shafa ya hada da kwamandoji da sauran manyan sojoji, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.
Nwachukwu ya ce an tura Manjo janar Godwin Umelo hedkwatar tsaro, DHQ daga cibiyar tsaro ta DSC a matsayin darekta janar na binciken harkokin tsaro da cigaban yaki, DRDB.
Asali: Legit.ng