Duniya kenan: Yadda aka kama wani mutum da ke cin hanjin 'yan adam a Zamfara
- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta kame wasu mutane da ke sace yara suna kashewa tare da cire hanji da makogwaronsu
- Bayan bincike, an gano inda suke sayarwa, an kamo mutumin da aka ce shi yake saye yana cin hanjin mutane
- 'Yan sanda na ci gaba da bincike, inda suka ce ba za su fadi komai kan lamarin ba har sai an gama bincike
Jihar Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara na gudanar da bincike kan wani dillalin motoci mai suna Aminu da ake zargin yana cin hanjin mutane.
Kama wanda ake zargin ya biyo bayan kama wasu mutane biyar da ‘yan sanda suka kama da zargin kashe wasu yara, Leadership ta ruwaito.
A wani faifan bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta mutanen sun yi ikirarin cewa suna garkuwa da yara tare da kashe su.
A wani bincike da aka yi a babban ofishin ‘yan sanda na Gusau, daya daga cikin wadanda ake zargin ya yi ikirarin kashe yara biyu tare da cire musu hanji da makogwaronsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
“Mun bayar da hanjin da makogwaron ga mai saye, akan kudi N500,000 ga kowane yaro.”
Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa shi maraya ne, amma da aka tambaye shi ko ya taba yin nadamar abin da ya aikata, sai ya ce a’a.
Daga bisani ‘yan sandan sun kamo mutumin da ya yi ikirarin cewa yana karbar hanji da makogwaron yana ci.
‘Yan sanda suna tsare da dukkan wadanda ake zargin domin ci gaba da yi musu tambayoyi saboda ‘yan sandan sun ki bayyana komai a batun har sai an kammala bincike, kamar yadda kafar Reuben Abati ta tattaro.
Mata ta kai karar TikTok saboda samun matsalar kwakwalwa tsabar kallo a kafar TikTok
A wani labarin, wata mata da ke bitar bidiyo a dandalin bidiyo na TikTok ta kai kara kotu saboda ta haddasa mata wani ciwon kwakwalwa da aka fi sani da Post Traumatic Stress Disorder (PTSD).
Matar, ta ce ta sami ciwon ne saboda aikinta shine duba bidiyon da suka hada da zane-zane, abubuwan tashin hankali da ka'idodin makirci da sauran 'hotuna masu tayar da hankali.'
Candie Frazier, wacce ke zaune a Las Vegas kuma 'yar kwangila ga tushen kamfanin TikTok, ByteDance, ta ce ita da sauran masu bitar galibi suna bata sa'o'i 12 kowace rana suna kallon bidiyoyi masu ban tsoro a kan dandamalin.
Asali: Legit.ng