An kuma: 'Yan bindiga sun sake yin awon gaba da jami'in kwalejin Zamfara
- 'Yan bindiga sun sake sace wani jami'in kwalejin ilimi na Gusau mai suna Bashiru
- Maharan sun yi garkuwa da ma'aikacin kwalejin ne a gidansa da tsakar daren ranar Talata
- Hakan na zuwa ne kwana guda bayan sakin matar wani lakcara da yaransa mata su biyu bayan an biya kudin fansa
Zamfara - Tsagerun 'yan bindiga sun sake yin garkuwa da wani mutum mai suna Bashiru wanda ya kasance jami'i a kwalejin ilimi na Gusau.
Channels TV ta rahoto cewa an yi garkuwa da jami'in ne a gidansa da ke Kortorkorshi da misalin karfe 1:00 na tsakar dare sannan aka tafi dashi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
An tattaro cewa Bashiru na daya daga cikin jami’an da ke sarrafa bayanai na kwalejin amma yana zama ne a wajen kwalejin.
Yanzu-Yanzu: An tsinci gawar babban ma'aikacin man fetur bayan iyalansa sun biya N5m ga masu garkuwa
Garkuwa da aka yi da Bashiru na zuwa ne sa’o’i 24 bayan an saki matar wani malami da ‘ya’yansa mata biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani ma’aikacin makarantar da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu.
Ya ce:
"Da gaske ne cewa an yi garkuwa da wani ma'aikacin kwalejin a gidansa da ke Kortokoshi wajen garin Gusau, babbar birnin jihar ta Zamfara."
A cewar ma'aikacin, an sace jami'in ne a ranar Talata a gidansa.
Zuwa yanzu wadanda suka yi garkuwa da shi basu nemi a biya kudin fansa ba, rahoton Independent.
Da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Shehu Muhammad ya ce basu samu damar tabbatar da lamarin ba amma zai yi jawabi daga baya.
Yan bindiga sun sako mata da 'ya'yan lakcara bayan sun karbi miliyoyi
A gefe guda, mun kawo a baya cewa yan bindiga sun sako mata da kuma ƴaƴa mata biyu na lakcaran kwalejin ilimi da fasaha dake Gusau, jihar Zamfara, Dakta Abdulrazak Muazu, bayan sun karbi kudin fansa.
Punch ta rahoto wani daga cikin iyalan gidan malamin, Muhammed Bello, yace yan bindigan sun sako su ne da safiyar Litinin, bayan sun amince su karbi miliyan N10m a matsayin fansa.
Da farko, bayan yan bindigan sun sace iyalan malamin kwalejin, sun nemi a biya miliyan N50m a matsayin fansa, amma daga baya suka sakko zuwa miliyan N10m.
Asali: Legit.ng