Da karshe: Gwamnatin Kano ta samar da hanyar sufuri da za ta maye a daidaita sahu
- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana irin matakin da ta dauka game da shiga yajin daikin da 'yan a daidaita sahu suka shiga
- Gwamnati ta ce za ta samar da ababen hawa domin kawo gurbin da zai maye 'yan adaidaita sahu a fadin jihar
- Hakazalika, ta ce batun biyan haraji na nan daram, don haka ba za ta janye ba, kuma dole 'yan adaidaita su yi rajista
Jihar Kano - Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin jihar Kano za ta sharewa mazauna jihar hawaye ta hanyar kaddamar da sabon tsarin sufuri biyo bayan yajin aikin 'yan a daidaita sahu, Daily Nigerian ta ruwaito.
Manajan daraktan hukumar KAROTA, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan yajin aikin da masu tuka a daidaita sahu a jihar suka yi.
A cewar Baffa:
“Gwamnati za ta kaddamar da sabon tsarin sufurin ne saboda muna son a duba yadda ake tafiyar da harkokin sufuri kamar yadda ake yi a yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Tuni dai shirye-shirye sun kai ga samar da ababen hawa.
Hakazalika, Baffa ya yi sharhi kan yadda gwamnatin a baya ta sanya kudin rajistar aiki ga 'yan a daidaita a kan kudi N100,000 amma daga baya ta sassauta zuwa kasa da haka
Ya kuma bayyana cewa, duk wadanda suka ki biyan kudin rajistar basa son bin doka ne, don haka gwamnati ba za ta yi shuru ta zuba musu ido ba.
Baffa ya ce ta bangarensa bai isa ya saka su dawo aiki ba, amma gwamnati na da damar samar da mafita ga al'ummarta
Mista Babba-Dan’agundi ya ce gwamnati ta damu da tsaro ne ba wai batun kudaden shiga ba.
Premium Times ta rahoto yana cewa:
"Wasu daga cikinsu suna ci gaba da aikata laifuka tare da masu a daidaita sahu, ba sa son yin rajista."
Ya ce batun ya je wurin gwamna Ganduje, kuma tuni ya ba da umarnin fara shirin
KAROTA ga 'yan daidaita sahun da suka shiga yajin aiki: Za ku gane shayi ruwa ne
A bangare guda, jim kadan bayan da kungiyar direbobin a daidaita sahu ta sanar da tsundumawa yajin aiki a jihar Kano, KAROTA ta yi martani mai zafi, inda ta nuna bacin ranta ga yadda lamarin yajin ya kasance.
Shugaban KAROTA Baffa Babba Danagundi ne yayi martani kan yajin aikin a ranar Litinin 10 ga watan Janairu, kasa da sa'o'i 24 da shiga yajin aikin.
Gidan radiyon Freedom ya bayyana cewa, Baffa ya bayyana a shirin Barka da Hantsi na gidan radiyon, inda ya yi martani da cewa, lallai matuka a daidaita sahu za su gane shayi ruwa ne.
Asali: Legit.ng