Jami’ar Kano Ta Ɗage Yin Jarrabawa Saboda Yajin Aikin Masu Baburan A-Daidaita-Sahu
- Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano ta dage jarrabawar dalibanta da aka shirya yi a ranakun Litinin da Talata da karfe 8 zuwa 11 na safe
- Shugaban kwamitin jarrabawa na jami'ar, Dr Yau Datti ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi yana mai cewa an dauki matakin ne sakamakon yajin aikin masu adaidaita sahu wanda dalibai da dama suka dogara da su don zuwa makaranta
- Amma Dr Yau ya ce za a rubuta jarrabawar da aka shirya yi karfe 11.30 - 2.30 da kuma a kare 3.00 - 6.00 na yamma, sannan daga bisani za a sanar da ranar rubuta wadanda aka dage
Jihar Kano - Jami'ar Yusuf Maitama Sule, Kano ta dage dukkan jarrabawar da a farko ta shirya yi karfe 8 zuwa 11 na safen ranakun Litinin da Talata 10 da 11 ga watan Janairun shekarar 2022.
Daily Trust ta rahoto cewa jami'ar ta sanar da hakan ne cikin wata takarda da shugaban kwamitin jarrabawa na jami'ar, Dr Yau Datti ya fitar a ranar Lahadi.
Masu baburan adaidaita sahu a sassan jihar sun fara yajin aiki kan abin da suka kira tsawalla musu biyan kudaden haraji ga hukumar kula da cinkoson ababen hawa na Kano, KAROTA.
Bayan taron gaggawa da mahukunta a jami'ar suka yi, sun dauki matakai kamar haka:
"Dukkan jarrabawar da aka shirya yi a yau Litinin 10 ga watan Janairun shekarar 2022, an dage su, kuma dukkan jarrabawar da aka shirya yi karfe 8-11 na safen ranar Talata 11 ga watan Janairun 2022, suma an dage su.
"Amma dukkan jarrabawar da aka shirya yi karfe 11.30 - 2.30 da kuma na karfe 3.00 - 6.00 na yamma duk za a gudanar da su."
Jami'ar za ta taimaka wa dalibai da manyan motoccinta na bus
Sanarwar ta kara da cewa jami'ar ta amince a fitar da manyan motoccinta na bus da za a tura su wasu tituna domin taimakawa dalibai zuwa makaranta da komawa gida, rahoton Daily Trust.
Har wa yau, jami'ar ta ce dukkan jarrabawar da aka dage su za a sanar da ranaku da lokacin da za a gudanar da su a nan gaba.
Tunda farko, Daily Trust ta ruwaito cewa dubban mutane suna ta tattaki a titunan Kano, wasu kuma sun rasa yadda za su yi saboda yajin aikin na masu baburan adaidaita sahu.
Masu adaidaita-sahu a Kano sun tsinduma yajin aiki saboda harajin N100
A baya ma, lamari mai kama da wanan ya taba faruwa inda fasinjoji a birnin Kano sun shiga mawuyacin hali saboda yajin aikin da masu adaidaita-sahu suka fara a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.
Sun fara yajin aikin ne domin nuna rashin amincewarsu da harajin N100 a kullum da gwamnatin jihar ta kakaba musu ta hannun Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa, KAROTA, da wasu batutuwan.
Masu adaidaita-sahun sun ce wannan matakin da suka dauka ya zama dole saboda abinda suka kwatanta da kwace da sunan haraji da wasu tarar da aka karba a hannunsu.
Asali: Legit.ng