Atiku ya aike da muhimmin sako ga hukumomin tsaro kan kisan mutum 200 a Zamfara

Atiku ya aike da muhimmin sako ga hukumomin tsaro kan kisan mutum 200 a Zamfara

  • Atiku Abubakar ya jajantawa al'umma da gwamnatin jihar Zamfara bisa kisan gillan da yan bindiga suka yi wa mutane a jihar kwanan nan
  • Tsohon mataimakin shugaban yace lamarin ya yi muni sosai kuma ya kai maƙura wajen tausayi da imani
  • Atiku ya bukaci hukumomin tsaron ƙasar nan su ƙara zage dantse wajen kare rayuwar al'umma

Zamfara - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna rashin jin daɗinsa bisa kisan mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba a Zamfara.

Atiku ya jajantawa iyalan waɗan da kisan kiyashin yan bindiga na kwanan nan ya shafa, a wani rubutu da yi yi a shafinsa na Facebook.

Atiku Abubakar
Atiku ya aike da muhimmin sako da hukumomin tsaro kan kisan mutum 200 a Zamfara Hoto: Atiku Abubakar FB Fage
Asali: Facebook

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin PDP ya kuma yi kira ga jami'an tsaron ƙasar nan su kara matsa ƙaimi wajen kawo karshen yan ta'adda a Najeriya.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sabon rahoto ya fallasa yadda Hafsoshin soji suka wawure dala biliyan $15bn kudin makamai

Atiku yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina miƙa sakon ta'aziyyata da jaje ga gwamnati da kuma al'ummar jihar Zamfara bisa kisan kiyashin da akai wa mutane ranar 6 ga watan Janairu, 2021, a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka."
"Abun da karayar zuciya da takaici jin labarin kashe dandazon mutane, waɗanda ba su ji ba kuma ba su gani ba a rana ɗaya. Mummunan lamarin ya fi karfin a kwatanta shi."

Atiku ya aike da sako ga jami'an tsaro.

Bayan haka, tsohon mataimakin shugaban ya ƙara da cewa duk da ya jajantawa mutanen da abin ya shafa, yana kuma kira ga jami'an tsaro su tashi tsaye.

"Ina mai ƙara jajantawa mutane da iyalan ƙauyukan da harin ya shafa yayin da suka gudanar da jana'izar yan uwansu.
"Ina kuma fatan hukumomin tsaro su tashi tsaye wajen samar da tsaro, domin mutane su rayu cikin kwanciyar hankali,"

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Daga ƙarshe, Atiku Abubakar, ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa waɗan da suka mutu, kuma yasa Aljanna ta zama makomar su.

A wani labarin kuma Wata Amarya ta koma ga Allah kwanaki kaɗan bayan shiga dakin mijinta a jihar Kano dake arewacin Najeriya

Fatima Balarabe, ta rasu ne bayan wata daya da kwana biyar da fara rayuwar aurenta, wanda aka ɗaura a watan Disamba, 2021.

Mahaifinta, Balarabe A. Haruna, ya yi godiya ga Allah bisa ni'imar da ya masa na ba shi ɗiya kamar Fatima, tare da addu'ar Allah ya jikanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262