Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sako mata da 'ya'yan lakcara bayan sun karbi miliyoyi

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sako mata da 'ya'yan lakcara bayan sun karbi miliyoyi

  • Matar lakcaran kwalejin fasaha dake Gusau, jihar Zamfara da yayansa mata biyu da aka sace sun kubuta daga hannun yan bindiga
  • Wani mamba daga cikin iyalan lakcaran ya bayyana cewa yan bindigan sun karbi miliyan N10m a matsayin kudin fansa
  • A ranar Jumu'a da daddare, wasu yan bindiga suka haura gidan Dakta Abdulrazak da nufin garkuwa da shi, amma ba su same shi ba

Zamfara - Yan bindiga sun sako mata da kuma ƴaƴa mata biyu na lakcaran kwalejin ilimi da fasaha dake Gusau, jihar Zamfara, Dakta Abdulrazak Muazu, bayan sun karbi kudin fansa.

Punch ta rahoto wani daga cikin iyalan gidan malamin, Muhammed Bello, yace yan bindigan sun sako su ne da safiyar Litinin, bayan sun amince su karbi miliyan N10m a matsayin fansa.

Kara karanta wannan

Halifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tahir Bauchi, da manyan Maluma sun taru a Kano don addu'a

FCET Gusau
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sako mata da 'ya'yan lakcara bayan sun karbi miliyoyi Hoto: fcetgusau.edu.ng
Asali: UGC

Da farko, bayan yan bindigan sun sace iyalan malamin kwalejin, sun nemi a biya miliyan N50m a matsayin fansa, amma daga baya suka sakko zuwa miliyan N10m.

Maharan sun sace matar malamin, Binta Jabaka, da ƴaƴansa mata biyu, Maryam Abdurrazak da Hafsat Abdurrazak, a gidansu dake ƙauyen Mareri, kusa da garin Gusau, da tsakiyar dare ranar Jumu'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda yan bindiga suka sace mutanen

Wani malamin kwalejin, Mohammed Lawal, ya shaida wa manema labarai cewa yan bindigan sun shiga gidan Dakta Abdurrazak ne da nufin sace shi.

Amma ba su sami nasarar ganin sa ba, domin ya boye a cilin din gidan lokacin da ya ji motsin shigowarsu, a cewar Lawal.

Vanguard ta rahoti shi Yace:

"Maharan sun tsallaka cikin gidan Dakta Abdulrazak ta katanga domin su yi awon gaba da shi, amma ya kubuta ta hanyar buya a cilin."

Kara karanta wannan

Sarkin Kano, Manyan Malamai, daruruwan mutane sun halarci Jana'izar Sheikh Ahmad Bamba

"Sun jima suna bincika gidan na tsawon awa ɗaya suna neman shi, amma da suka tabbatar ba zasu gan shi ba, sai suka sace matarsa Binta da ƴaƴansa mata biyu, Hafsat da Maryam."

A wani labarin na daban kuma Gwamna ya fallasa sunayen mutum 19 da ake nema ruwa a jallo a jiharsa

Gwamnan Ribas ya bayyana sunayen wasu mutum 19 dake da hannu a gudanar da haramtacciyar matatar ɗanyen man fetur a jiharsa.

Gwamna Wike ya bayyana su a matsayin masu aikata babban laifi da ake nema, kuma yace jami'an tsaro za su kame su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262