Yadda Kano ta rasa ‘Yan siyasa, ‘Dan kasuwa, Saraki, Malami, da wasu manya 8 a kwana 53

Yadda Kano ta rasa ‘Yan siyasa, ‘Dan kasuwa, Saraki, Malami, da wasu manya 8 a kwana 53

  • Rahoton 21stcenturychronicle ya nuna akalla shahararrun mutane takwas suka rasu daga karshen shekarar bara ta 2021 zuwa cikin makon nan
  • Daga cikin wadanda suka rasu akwai gawurtattun ‘yan kasuwa, jagororin al’umma, ‘yan siyasa, malaman addini, tsofaffin ma’aikatan gwamnati
  • A karshen shekarar bara irinsu Sani Dangote, da mutumin da ya fi kowa dadewa a majalisar masarautar Kano, Sarkin Bai Adnan Muktar suka rasu

1. Sani Dangote

Wanda ya fara mutuwa shi ne Sani Dangote a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2021. Marigayin shi ne mataimakin shugaban kamfanin nan na Dangote Group.

2. Sani Buhari

Bayan kanin Alhaji Sani Dangote sai aka ji mutuwar wani dattijon takwaransa a karshen Nuwamba, Alhaji Sani Daura wanda ya rasu kasar UAE.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Shugaban Jam’iyya Ya Dauki Mataki ba da Sanin Sauran Shugabannin APC ba

3. Adnan Mukhtar

A ranar 3 ga watan Disamba, 2022, Sarkin Ban Kano, Adnan Mukhtar ya rasu a shekara 95. Tsohon hakimin na Danbatta ya na masarautar Kano tun 1956.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

4. Ado Gwaram

Ado Gwaram wanda ya mutu a irin wannan rana a Disamba ya rike sakataren gwamnatin jihar Kano sau biyu – 1988 zuwa 1991, da kuma 1999 zuwa 2003.

Kano ta rasa manya
Wadanda suka rasu a Kano Hoto: /21stcenturychronicle.com
Asali: UGC

5. Inuwa Musa Kwankwaso

Bayan kwana 17 sai Kanawa suka tashi da labarin mutuwar Kwamred Inuwa Musa Kwankwaso. ‘Danuwan tsohon gwamnan ya bar Duniya ya na da shekara 64.

6. Datti Ahmad

A ranar 30 ga watan Disamban 2021, jihar Kano ta rasa tsohon ‘dan siyasa, Dr. Ibrahim Datti Ahmad wanda ya taba zama shugaban majalisar shari’a ta kasa.

7. Bashir Othman Tofa

Tsohon ‘dan takarar shugaban kasa, Alhaji Bashir Othman Tofa ya rasu a ranar 3 ga watan Junairun 2022 bayan ya yi fama da jinya, dattijon ya rasu a shekara 74.

Kara karanta wannan

Kwankwaso @66: Wasu abubuwa 10 da ba ka sani ba a game da ‘Dan Takaran NNPP

8. Ahmad Ibrahim Bamba

A ranar 7 Juma’a ga watan Junairun 2022, Duniyar musulunci tayi rashin babban malami Dr. Ahmad Ibrahim Bamba wanda tun 1991 yake koyar da ilmin addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng