Farmakin Zamfara: An samo gawawwaki 143 yayin da aka cigaba da neman wasu

Farmakin Zamfara: An samo gawawwaki 143 yayin da aka cigaba da neman wasu

  • An samo a kalla gawawwakin mutane 143 a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum sakamakon barnar da yaran Bello Turji suka yi a yankunan
  • Mazauna yankin sun sanar da cewa, an ga wasu gawawwakin a daji inda aka sassara su yayin da aka kone wasu har ba a iya gane su
  • Abun takaicin shi ne yadda 'yan ta'addan suke kone gidajen mutane kuma suka hana mata da kananan yara fitowa har sai sun yi kurmus

Zamfara - A kalla gawawwaki 143 aka samo kuma aka birne sakamakon kisan gillar da 'yan ta'adda suka yi a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a ranakun Laraba da Alhamis a jihar Zamfara, Daily Trust ta tattaro.

Idan za mu tuna, 'yan ta'adda masu gudun hijira kuma yaran Bello Turji, wadanda suke gudun hijira sakamakon luguden jiragen NAF a dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi, suna hanyarsu ta hijira ne suka dinga kashe mutane.

Kara karanta wannan

Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji

Zamfara: An samo gawawwaki 143 yayin da aka cigaba da neman wasu
Zamfara: An samo gawawwaki 143 yayin da aka cigaba da neman wasu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Mazauna yankin sun sanar da Daily Trust cewa an samo gawawwakin daga daji sabda 'yan ta'addan sun ritsa jama'a yayin da suke gonakinsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an sassara wasu gawawwaki yayin da aka kone wasu ta yadda ba a gane su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin yankin mai suna Babangida, ya ce:

"Daya daga cikin miyagun labaran shine yadda basu tsahirta wa mata da kananan yara ba. A yayin da suka sanya wa gidaje wuta, yara da mata ba a bar su sun tsere ba saboda 'yan ta'addan sun tsaya suna jiran ganin wanda zai fito.
"Daga bisani aka kwaso gawawwakin konannun mutane aka birne. Wadanda suka tsere sun samu mafaka a wasu yankuna. A gaskiya wannan babban bala'i ne.
“Yankunan da aka yi wa barnar sun fi goma. Hakan ta faru ne saboda 'yan bindigan na kan hanya ne. Duk da sun tafi, amma suna kusa da kauyukan da suka yi wa barna," yace.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60

Turji, gagararren ɗan bindigan Zamfara ya sauya sheƙa saboda luguden sojoji

A wani labari na daban, Bello Turji, gagararren dan bindigan da ya addabi yankin arewa maso yamma, ya sauya sheka daga jihar Zamfara sakamakon tsananin luguden wutar da sojojin Najeriya ke yi musu.

Daily Trust ta ruwaito yadda sojojin saman Najeriya suka ragargaza sansanonin 'yan bindiga a samamen da suke ta kaiwa yankin.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, gagararen dan bindigan da mutanensa sun hanzarta barin dajin da suke saboda jiragen NAF suna ta ragargazar dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi kuma suna tafiya kudancin Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng