Obasanjo ya bayyana hanyar magance rashin aikin yi ga matasan Najeriya
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce a siyasance ya dace a yi amfani da dabara wurin shawo kan matsalar matasa marasa aikin yi
- Obasanjo ya ce babu shakka yawan jama'a a kasa da aka kasa sarrafa ta abun firgici ne, ballantana mai matasa da yawa
- Fitaccen dan siyasar ya ce, hanyar tabbatar da zaman lafiya ita ce dakile duk wata kafa da za ta bai wa matasa damar tada hankula da aikata laifuka
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce mayar da hankali da kuma aiki shi ne zai iya mayar da yawan jama'ar kasar nan zuwa masu amfani.
A yayin jawabi ranar Juma'a da wani taro a Legas, Obasanjo ya nuna damuwarsa kan yadda yawan jama'a ke hauhawa a kasar nan, ballantana matasa marasa aikin yi, TheCable ta ruwaito.
Tsohon shugaban kasan yace ganin yawan rashin aiki yi da kuma gazawar kasar nan wurin lamurran mulki, matasa masu yawa sun fada harkar tada hankula da garkuwa da mutane.
"Tambayoyi na farko su ne: Ta yaya za mu ciyar da mutanen nan? Ta yaya zamu samar musu da muhalli, ta yaya zasu samu ilimi? Matukar akwai tsaro da sauransu ai ba matsala bane," yace.
"Jerin tambayoyi na biyu su ne: Ta yaya zamu kiyaye yawan zugar matasa marasa aikin yi? Ta yaya za mu hana su shiga kungiyoyin tada hankula da kuma kungiyoyin masu garkuwa da mutane?
“Yawan mutane da ba a iya sarrafa su abun tsoro ne
"Wannan ne ya bayyana a matsayin hanyar shawo kai. Aiki a siyasance zai iya sa yawan mutane ya zama mai amfani, ina ga wannan ita ce mafita."
An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su
Tsohon shugaban kasa ya ce akwai tsarikan da kasashe ya dace su yi amfani da su wurin inganta yawansu tare da mayar da shi mai amfani, TheCable ta ruwaito.
2023: Najeriya na bukatar wanda zai kawo hadin kai kamar Atiku, Dokpesi
A wani labari na daban, Raymond Dokpesi, tsohon shugaban kafar sadarwa ta Daar ya ce ya kamata shugaban kasan da zai gaji mulki a 2023 ya kasance wanda zai hade kan kasar, TheCable ta ruwaito.
Dokpesi ya ce Najeriya ba ta taba rabuwa ba, inda ya kara da cewa kasar nan ta na bukatar mutum kamar Atiku Abubakar ne, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya mulki kasar yadda ya dace.
“Yanzu da 2023 ta ke karatowa, tattalin arzikin kasar ya tabarbare gaba daya kuma yaranmu sun rasa ayyukan yi,” a cewarsa.
“Gaskiya mu na bukatar wanda zai hade kan kasa, tsayayyen mutum, wanda ya san kan dukiya don samun damar rike kasar nan da kyau kamar Atiku.”
Asali: Legit.ng