Ka fadawa duniya wa ya kashe Ahmed Gulak: Sanata ya kalubalanci gwamna kan kisan jigon APC
- Rochas Okorocha a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, ya zargi gwamnan jihar Imo da hannu a kisan Ahmed Gulak a Owerri, jihar Imo
- Tsohon gwamnan ya ce Hope Uzodinma yana da rundunar masheka da ta hada da jami’an ‘yan sanda, SSS, sojoji da Ebubeagu.
- A cewar Okorocha, rundunar ta gwamnan ita ce ke da alhakin kashe shugabannin gargajiya da kuma haddasa rashin tsaro a jihar Imo
Jihar Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya tona batun kisan gillar da aka yi wa jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Ahmed Gulak a Owerri, jihar Imo.
Okorocha a lokacin da yake ba da labarin mutuwar Gulak da aka kashe a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Sam Mbakwe, jihar Imo a ranar 30 ga Mayu, 2021, ya zargi gwamnan, Hope Uzodinma da wata tawagar mashekansa.
Jaridar This Day ta rahoto cewa sanatan ya yi zargin cewa gwamnan jihar Imo ne ya kafa rundunar masheka da ya kira da Hopism Strike Force (HSF) kuma rundunar ita ce ke da alhakin duk wasu kashe-kashe da tashe-tashen hankula a jihar.
A cewar Okorocha, mambobin tawagar HSF sun hada da jami’an soja, jami’an tsaro ta SSS, ‘yan sandan da kuma WASU Ebubeagu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Okorocha ya Kalubalanci Gwamna Hope Uzodinma
A ci gaba da zarge-zargen da ya yi wa gwamnan, Okorocha ya bukaci Uzodinma da ya fito fili ya bayyana masu daukar nauyin tashe-tashen hankula a jihar.
Okorocha ya ce:
"Idan gwamnan ya san ba shi da irin wannan runduna a jihar, to ya shaida wa duniya wanda ya kashe Gulak."
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya ce batunsa ba shi da dangantaka da bacin rai bisa irin halin kuncin da gwamnatin ta sa surukinsa, Uche Nwosu.
Yace:
"Ina so in maimaita wannan Sheba, CSO din Uzodimma, yana tsare tsawon kwanaki 4 da suka gabata. Yana cikin rundunar Uzodimma da ke aikata barna, har yanzu ina tambayar Uzodimma, wa ya kashe Gulak?"
“Wa ya kashe sarakunan gargajiya? Wane ne ya kashe mutanen Imo kusan 140 da aka gano a dakin ajiyar gawarwaki?
"Hope Uzodimma na da wata gagarumar runduna mai suna 'Hope Striking Force' a tambaye su ko me suke yi da wannan tawagar masheka."
A tun farko, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige Ahmed Gulak, tsohon mai bada shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Owerri, jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.
Gulak, jigo a jam'iyyar All Progresive Congress, APC, ya baro Owerri ne yana hanyarsa na komawa Abuja a daren ranar Asabar yayin da yan bindigan suka kashe shi.
A cewar jaridar Tribune, tsohon abokinsa da suka yi makaranta tare, Dr Umar Ado ne ya bada sanarwar rasuwarsa a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng