Babbar magana: Ana kukan rashin aikin yi, gwamnatin Buhari za ta rage ma'aikata
- Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin tarayya na shirin rage yawan ma'aikatanta
- Hakan ya haifar da tashin hankali da fargaba a tsakanin ma'aikatan tarayya
- Sai dai kuma ministar kudi ta ce akwai tanadi na musamman da gwamnatin tarayya ta yi wa wadanda abun zai shafa
Abuja - Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun shiga tashin hankali a ranar Laraba yayin da gwamnatin tarayyar ta bayyana shirinta na rage yawan ma'aikatanta.
Tuni dai gwamnati ta fara shirin tanadarwa ma'aikatan da abun zai shafa wani kunshin sallama na musamman.
Sai dai kuma, an samu 'yar hatsaniya yayin da kungiyar kwadago ta bayyana shirin sallamar ma'aikatan a matsayin koma baya ga shirin daukar ma’aikata da gwamnatin tarayya ta yi ta tallatawa.
Ministar kudi, Misis Zainab Ahmed ta ce ya zama dole a rage girman gwamnati saboda makudan kudaden da gwamnati ke kashewa a duk shekara, Sahara Reporters da The Nation suka rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ana fargabar cewa hade hukumomin da ake shirin yi zai kara tabarbarewar matsalar rashin aikin yi a kasar.
Sai dai kuma, ministar tace tsarin da gwamnati za ta bi wajen rage yawan ma'aikatan ba zai kasance daidai da rahoton Stephen Oronsaye ba.
Ta ce gwamnati na aiki kan "kudin sallamar" da za a biya wadanda abun zai shafa.
Misis Ahmed ta ce:
"Akwai kwamiti na musamman, karkashin jagorancin babban sakataren gwamnati da ke aiki a kan bitar hukumomin, da nufin ruguza su ta hanyar amfani da rahoton Oransanye. A karshe, abin da muke son yi shi ne a rage girman gwamnati da kuma rage yawan kudin ma’aikata sannan daga cikin tanadin shine bayar da kudin sallama mai tsoka.”
Da take bayanin dalilin da ya sa ake shirin sallamar, ministar kudin ta ce:
“Muna fuskantar kalubale na kudaden shiga. Saboda haka, duk abin da muke yi, ba za mu iya bayar da kudin sallama ba idan ba ku son karbarshi nan take. Saboda haka, lokacin da kuke neman mutane su tafi, dole ne ku tanadar masu wannan kunshi na sallama."
Ta kara da cewa:
"Akwai abubuwa da dama da ke faruwa. Wadannan ba hukunci mai sauki bane saboda sun shafi mutane da iyalai. Don haka, ya zama dole mu tabbatar da cewar duk abin da muka yi alkawari a zahiri za mu isar da shi”.
Mai dakin Buhari ta canza masu rayuwa, tayi wa masu nakasa hanyar samun aiki mai-tsoka
A wani labarin, mun ji cewa mai girma Aisha Muhammadu Buhari, ta sa hannu wajen samawa wasu Bayin Allah biyu da suka kammala bautar kasa watau NYSC aikin yi.
A ranar Alhamis, 6 ga watan Junairu, 2022 ne jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Aisha Muhammadu Buhari ta taimakawa wadannan mutane.
Wadannan Bayin Allah; Onogberie Efe Lulu da Nuruddeen Tahir, su na fama da nakasar halitta.
Asali: Legit.ng