Buhari: Ba na jin dadin halin da wutar lantarkin Najeriya ke ciki
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadinsa a kan matsalar wutar lantarkin Najeriya
- Najeriya ta na da damar samar da wutar lantarki, megawatts 13,000 amma yanzu haka tana samar da megawatts 4,000
- Dama a watan mayun 2018, shugaban kasa ya caccaka akan kashe dala biliyan 16 a kan wutar lantarki lokacin mulkin Olusegun Obasanjo
Shugaban kasa Muhammadu ya nuna rashin jin dadinsa akan halin da wutar lantarkin Najeriya take ciki.
Najeriya tana da damar samar da wutar lantarki megawatts 13,000 yanzu haka, kasar da ta fi ko wacce yawan jama’a a Afirka tana samar da megawatts 4,000 kacal a tashar wutar lantarki.
A watan Mayun 2018, shugaban kasa ya caccaki yadda mulkin tsohon shugaban Olusegun Obasanjo ya ke amfani da dala biliyan 16 saboda wutar lantarki.
Sai dai yayin tattaunawarsa a gidan talabijin din Channels ranar Laraba, Shugaban kasa ya ce mulkinsa a shirye yake da ya gyara kasar nan tare da samar da ingantacciyar wutar lantarki.
Bayan an tambaye shi akan idan yana murna akan yanayin wutar lantarkin da kasar nan ke samarwa, shugaban kasa ya ce ba ya jin dadin hakan.
“Gaskiya ba na jin dadi saboda babu wata kasar da zata ci gaba ba tare da kayan more rayuwa ba da wutar lantarki,” a cewar Buhari.
“Gwamnati tana kokari akan titina. Kalli abinda ke faruwa tsakanin Legas zuwa Ibadan a watanni 6 na baya da kuma yanzu.
“Yanzu muna gyaran titin jirgin kasa ne daga Legas zuwa Kano, sai kuma daga nan zuwa Kaduna zuwa Kano. Don haka ya kamata mu samar da kayan more rayuwa yadda kowanne dan Najeriya zai ci gaba da ayyukansa. Amma idan babu kayan more rayuwa, babu titina masu kyau, an kashe titinan jiragen kasa, babu wuta, me ake tunanin mutane su yi?”
Yayin da ya bayyana cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya, TCN dari bisa dari na gwamnati ne, ya ce gwamnatin ta gaji kamfanin raba auren DisCos.
A cewar shugaban kasa, “Masu su, su waye? Ba injiniyoyin wutar lantarki bane, ba su da kudi, kawai taimako ne na siyasa aka yi musu.”
Buhari: Abinda na sanar da Gwamnan Oyo yayin da ya ziyarce ni kan rikicin manoma da makiyaya
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda suka yi da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, wurin kawo tsarikan gargajiya domin shawo kan matsalar makiyaya da manoma, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Buhari ya ce gwamnoni biyu sun ziyarci Aso Rock kan rikicin, amma ya shawarce su da su yi kokarin komawa su shawo kan matsalar ta hanyar shugabannin gargajiya da kuma makiyayan da suke hana zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.
Shugaban kasan bai fadi sunan dayan gwamnan ba, amma Daily Trust ta tuna cewa jihohin Ondo da Ogun ne suke fuskantar matsalar makiyaya da manoma wanda hakan ya kawo asarar rayuka da kadarori.
Asali: Legit.ng