Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe
- Mayakan kungiyar ta'addanci ISWAP sun kai hari yankin garin Buni Gari, dake jihar Yobe da Asubahin ranar Laraba
- Mazauna yankin sun bayyana cewa yan ta'addan sun tarwatsa tawagar jami'an tsaro, sannan suka kona motar ɗaukar marasa lafiya
- A halin yanzun mutanen garin da lamarin ya shafa sun watsu cikin jeji domin tsira da rayuwar su
Yobe - Wasu yan ta'adda ake zargin mayakan ISWAP ne sun mamaye kauyen Buni Gari, dake karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan ta'addan sun kona motar asibiti ta marasa lafiya kuma suka kwashi magunguna suka yi awon gaba da su.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Laraba, 5 ga watan Janairu, lokacin da mutane ke gudanar da sallah ta subahi.
Wani mazaunin yankin, wanda ya bayyana sunansa da Muhammad Abubakar, yace yan ta'addan sun tarwatsa jami'an tsaron yankin yayin da mutane suka yi takan su domin tsira.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta rahoto Abubakar yace:
"Muna cikin matukar tashin hankali, ba mu san in da zamu nufa ba. Akwai babbar matsala domin an faɗa mana an ga motsin yan ta'addan a cikin daji. Mun mika komai ga Allah."
Yadda lamarin ya faru
Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace:
"Kusan karfe 5:50 na asuba muka fara jin karar harbin bindiga daga kowane bangare, nan take muka sanar da mutane suka gudu cikin jeji domin neman mafaka."
"Maharan sun kone asibitin mu, kafin daga bisani suka nufi wurin da jami'an tsaro suke a garin Buni Gari."
Me hukumomin tsaro suka ce game da harin?
Har zuwa yanzun da muka haɗa wannan rahoto, duk wani yunkurin jin ta bakin hukumomin tsaro daga yankin domin tabbatar da abin da ya faru ya ci tura.
A wani labarin na daban kuma Wani mutumi ya yi lalata da mata 10 a Hotel da sunan kwamishina a wata jiha
Yan sanda sun yi ram da wani mutumi bisa zargin amfani da sunan kwamishinan Akwa Ibom yana damfaran mutane.
Kakakin yan sanda na jihar, Odiko Macdon, yace wanda ake zargi ya kwanta da mata 10 bisa alkawarin zai taimaka musu su samu aiki.
Asali: Legit.ng