Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya nada sabbin jami'ai na hukumar gudunarwa ta NNPC
- Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabbin jami'ai na hukumar gudanarwar kamfanin NNPC
- Hakan ya kasance ne kamar yadda sashe na 59 (2) na dokar masana’antar mai ta 2021 ta bashi dama
- Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin jami'ai na hukumar gudanarwar kamfanin man fetur na kasa.
Hakan ya kasance ne bisa karfin ikon da yake da shi karkashin sashe na 59(2) na dokar masana’antar man fetur wanda ya saka hannu a ranar 16 ga Agusta, 2021.
Mai ba shugaban kasar shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu.
Ya bayyana Margret Okadigbo (Kudu maso Gabas) a matsayin shugabar hukumar; Mele Kyari a matsayin babban jami'in gudanarwa da kuma Umar Ajiya a matsayin babban jami'in kudi.
Sauran mambobin hukumar sune Dr Tajudeen Umar (Arewa maso Gabas), Lami Ahmed (Arewa ta Tsakiya), Mohammed Lawal (Arewa maso Yamma), Henry Obih (Kudu maso Gabas), Constance Marshal (Kudu maso Kudu), da Cif Pius Akinyelure (Kudu maso Yamma).
Har ila yau, an nada wasu manyan kwamishinoni na Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya.
Wadanda aka nada a wannan mukami sune; babban kwamishinan ci gaban hukumar, Dr Nuhu Habib (Kano); babban kwamishinan dokokin tattalin arziki da tsare-tsare, Dr Kelechi Ofoegbu (Imo).
Sai kuma babban kwamishinan lafiya, tsaro, muhalli da al'umma, Kyaftin Tonlagha John (Delta); da babban kwamishinan ayyuka da gudanarwa, Jide Adeola (Kogi).
Wadanda aka da farko sun hada da shugaban hukumar, jagora, babban kwamishinan bincike da gudanarwar filaye, da babban lwamishinan kudi da asusun ajiya.
Sabbin wadanda aka nada a hukumar kula da man fetur ta Najeriya sune, Francis Alabo Ogaree (Rivers), babban daraktan sarrafa sunadaren 'Hydrocarbon', Mustapha Lamorde (Adamawa), babban daraktan lafiya, tsaro, muhalli da al'umma.
Sauran sune Mansur Kuliya (Kano), babban daraktan asusun more rayuwa na Gas, Bashir Sadiq (Sokoto), babban daraktan ayyuka da gudanarwa, Dr Zainab Gobir (Kwara), babbar daraktan dokokin tattalin rrziki da tsare-tsare.
Sabbin mambobin hukumar kula da kayan mai na Midstream and Downstream Infrastructure Fund, sune Mista Effiong Abia (Akwa Ibom), Bobboi Ahmed (Adamawa), da Injiniya Abdullahi Bukar (Katsina).
Sabuwar dokar mai za ta ruguza aikin NNPC da PPPRA a Najeriya
A baya mun kawo cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin PIB na shekarar 2020 a gaban ‘yan majalisar tarayya.
Rahoton ya bayyana cewa wannan kudiri zai bada damar kafa sabon kamfanin man Najeriya. A dalilin haka kuma za a yi fatali da kamfanin man NNPC.
Idan wannan kudiri ya samu karbuwa kuma har ya zama doka, gwamnati za ta soke hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan mai a Najeriya.
Asali: Legit.ng