Duniya kenan: Yadda uwa ta haifi jariri a cikin jirgin sama ta jefar dashi bandakin jirgi
- Wata mata ta haifi santalelen jaririnta, amma ta jefar dashi a cikin jirgi saboda wasu dalilai da ba a sani ba
- Wannan lamari ya faru ne a wata kasa a nahiyar Afrika kuma tuni aka gano wacece wannan mata
- Yanzu haka dai an kwantar da ita da jaririn a asibiti kafin daga bisani a ci gaba da bincike kan wannan lamari
Mauritius - A yayin da ake gudanar da aikin bincike domin duba lafiyar jirgi na yau da kullum, jami'an filin jirgin sama a Mauritius sun gano wani jariri da aka jefar a cikin kwandon sharan ban daki na jirgin sama na Air Mauritius.
Ana zargin wata mata ‘yar Malagasy a kasar Madagascar mai shekaru 20 da haihuwar sabon jaririn, kuma an kama ta da farko, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara
Da farko dai ta musanta cewa yaron nata ne amma an yi mata gwaje-gwaje wanda ya tabbatar da cewa ta haihu, kamar Premium Times ta tattaro.
An garzaya da uwar da jaririn duka zuwa asibiti kuma hukumomi sun ce suna nan "lafiya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Matar 'yar Malagasy, wacce ta zo Mauritius a kan takardar izinin aiki na shekaru biyu, tuni aka sanya ta a karkashin kulawar 'yan sanda.
Za a yi mata tambayoyi bayan an sallame ta daga asibiti kuma za a tuhume ta da jefar da jariri, kamar yadda rahotanni suka ce hukumomin kasar sun yanke.
Jirgin na Air Mauritius, wanda ya taso daga birnin Madagascar a ranar 1 ga watan Janairu ya sauka a filin jirgin sama na Sir Seewoosagur Ramgoolam da ke wajen babban birnin Port Louis.
'Yan bindiga sun hallaka jariri dan wata uku tare da mutane da dama a Benue
A wani labarin, 'yan bindiga sun harbe jariri dan wata uku kacal har lahira tare da wasu mutum 12 a hari daban-daban a wasu kauyukan karamar hukumar Guma, jihar Benue, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yan bindigan sun bude wuta kan matafiya a hanyar Uikpam–Umenger da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Talata, inda suka kashe mutum biyar, cikinsu harda jariri, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Hakanan, sauran mutum 8 Din an kashe su ne a yankin Branch Ude da misalin Karfe 10:00 na daren ranar Talata (Jiya).
Asali: Legit.ng