Yanzu-Yanzu: Legas ta yi rashin mace ta farko mataimakiyar shugaban majalisa

Yanzu-Yanzu: Legas ta yi rashin mace ta farko mataimakiyar shugaban majalisa

  • Jihar Legas ta yi rashin wata fitacciyar 'yar siyasa, wacce ta kasance mace ta farko da ta rike mukamin mataimakiyar kakakin majalisa
  • Honorabul Adetoun Adediran ta rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda rahoto ya tabbatar
  • Ta rasu da sanyin safiyar yau Laraba 5 ga watan Janairun wannan shekarar, inji rahotanni daga Legas

Legas - Jaridar Independent ta ruwaito cewa, tsohuwar mataimakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Honorabul Adetoun Adediran ta rasu.

Adediran ta rasu ne da sanyin safiyar yau Laraba 5 ga watan Janairun 2022 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, inji rahoton The Gazelle News.

Jihar Legas ta yi rashin mataimakiyar kakakin majalisa
Yanzu-Yanzu: Legas ta yi rashin mace ta farko mataimakiyar shugaban majalisa | Hoto: naijanews.com

Adediran ita ce mace ta farko da aka zaba a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Legas lokacin da ta yi aiki tsakanin 1999 zuwa 2003.

Tun a wancan lokacin, ta rike mukaman siyasa da dama ciki har da kasancewarta shugabar mata na jam'iyyar APC reshen jihar Legas.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan daba sun kai farmaki gidan talabijin, sun raunata edita tare da lalata kayan aiki

Zuwa rasuwarta, Adetoun mamba ce a hukumar kula da ilimin firamare ta Michael Otedola.

Bashir Tofa, dan takarar shugaban kasa a zaben 1993, ya rasu

A wani labarin, Alhaji Bashir Tofa, daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a zaben 1993, wanda ake yi wa kallon zabe mafi adalci a Najeriya, ya rasu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyoyi daga yan uwansa, Tofa ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Aminu Kano, AKTH, a safiyar ranar Litinin bayan gajeruwar lafiya, The Cable ta ruwaito.

Da ya ke tabbatar da rasuwarsa, dan uwan marigayin ya ce, "Alhaji Bashir Tofa ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.