Daga karshe: Minista ya bayyana hanyar da Buhari zai bi wajen sakin Nnamdu Kanu

Daga karshe: Minista ya bayyana hanyar da Buhari zai bi wajen sakin Nnamdu Kanu

  • Ministan shari'a a Najeriya ya bayyana hanyoyin da Buhari zai bi kafin ya saki Nnamdi Kanu da aka tsare a 2021
  • Ya bayyana cewa, shugaba Buhari mutum ne da zai duba maslahar jama'ar Najeriya baki daya sabanin na daidaiku
  • Saboda haka, Malami ya yi bayanin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke duba lamurra kafin aiwatarwa

Abuja - Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a ranar Talata, 4 ga watan Janairu, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai duba maslahar 'yan Najeriya miliyan 200 wajen sakin Nnamdi Kanu.

Malami, yayin wata hira da yayi da manema labarai a ranar Talata, ya bayyana cewa wannan shine abin da shugaban kasa zai yi la’akari da shi kafin amincewa da bukatar shugabannin yankin kudu maso gabas na sakin Nnamdi Kanu shugaban IPOB, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

Nnamdi Kanu na tsare, amma da yiyuwar sakinsa
Daga karshe: Minista ya bayyana hanyar da Buhari zai bi wajen sakin Nnamdu Kanu | Hoto: punchng.com

Ya bayyana cewa dole ne shugaba Buhari ya duba yadda amincewa da bukatar zai samar wa ‘yan Najeriya sama da miliyan 200 kwanciyar hankali.

Ministan shari’a ya kara da cewa irin wannan la’akari shi ya yi tasiri wajen kin sanya hannu a kan dokar gyara kundin zabe da Buhari ya yi watsi da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Malami:

“Ta hanyar yin cikakken bayani game da batutuwa biyu da aka gabatar: batun da ya shafi dokar zabe da kuma batun Kanu har zuwa kan IPOB, abin da zan iya fada muku tabbas shi ne shawarar da Shugaban kasa ya yanke ne daidai kuma a kowane lokaci la'akari ne da maslahar jama'a.
“A fannin mulki da kuma abin da na zo na koya game da hankali da zuciyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, shi ne yakan dauki mutane miliyan 200 a maimakon mutane daidaiku.

Kara karanta wannan

An tara Malamai 2500 a Kano don addu'ar Allah ya ba Tinubu Shugabancin Najeriya

"Saboda haka, batun Kanu, abin da zai iya tafiyar da hukuncin shugaban kasa dangane da duk wata bukata da aka gabatar, shi ne maslahar jama'a sabanin wani yanki guda."

Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

Tun farko, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar yan ta'addan IPOB ya sabawa dokar da ta baiwa sashen Shari'a karfin cin gashin kanta.

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin manyan dattawan Igbo wanda ya hada da Tsohon Minista Sufurin Sama kuma tsohon dan majalisa, Chief Mbazulike Amaechi.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Buhari yace:

"Ka gabatar da bukata mai wuyan gaske a kaina matsayin Shugaban kasar nan...Tun da na zama shugaba shekaru shida da suka gabata babu wanda zai ce na yi shisshigi cikin aikin Shari'a."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

"Wannan bukata na da nauyin gaske. zan yi shawara."

A wani labarin, Hadakar kungiyoyin arewa (CNG) ta nuna kin amincewarta da bukatar shugabannin Ibo akan kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari na sakin shugabannin masu rajin kafa kasar Biafara (IPOB).

Daily Trust ta bayyana yadda shugabannin Ibo suka kai wa Buhari ziyara a ranar Juma’a har fadarsa suna bukatar sakin Kanu inda shugaban kasar yace bukatar tana da nauyi.

Amma CNG ta kwatanta bukatar tasu a matsayin hanyar juyar da adalci, inda suka ce a bi da duk wadanda suka bukaci hakan a matsayin masu hada kai da taimaka wa Kanu wurin cutar da al’umma, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.