Yan bindiga sun kashe mutum 7 yan gida daya, da wasu mutum 17 a sabon harin jihar Kaduna
- Wasu tsagerun yan bindiga sun hallaka mutum 7 yan gida ɗaya da wasu mutum 17 na daban a sabon harin da suka kai yankunan karamar hukumar Igabi
- Wani shugaban al'umma a yankin, Bello Musa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara tura dakarun soji zuwa Igabi
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, yace hukumomin tsaro sun isa wurin, suna aikin tabbatar da abin da ya faru
Kaduna - Miyagun yan bindiga sun kashe mutum 7 yan gida ɗaya a wani sabon hari da suka kai kauyen Sabon Birni, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya tabbatar da haka ga jaridar Channels tv.
Yace hukumomin tsaro na aiki tukuru domin tabbatar da abin da ya faru da kuma alƙaluman mutane da harin ya shafa.
Sai dai a cewar mutanen dake zaune a kauyen, lamarin ya faru ranar Litinin da daddare, lokacin da maharan suka shigo ƙauyen, suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane hali mutanen kauyen ke ciki bayan harin?
Wani shugaban al'umma a ƙauyen, Bello Musa, ya bayyana cewa mafi yawan mazauna ƙauyen sun tsere daga gidajen su saboda tsoron harin yan bindiga.
Musa ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta turo ƙarin sojoji zuwa yankunan Igabi da sauran sassan jihar Kaduna dake fama da ayyukan ta'addancin yan bindiga.
Premium Times ta rahoto mutumin yace:
"Muna kira ga gwamnatin tarayya ta kara turo karin sojoji yankin karamar hukumar Igabi, da sauran yankunan da matsalar tsaro ke kara kamari a Kaduna."
Yan bindiga sun sake kashe mutum 17
Haka nan kuma, wasu yan bindiga sun kai wani hari mai kama da wannan ƙauyuka 13 dake karkashin gundumar Kerawa, karamar hukumar Igabi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun kashe akalla mutum 17 yayin harin da suka kai waɗan nan ƙauyuka.
A cewar wani mazaunin yankin da abun ya shafa, yan bindigan sun kai hari waɗan nan kauyukan ne ɗaya bayan ɗaya.
Har zuwa yanzun da muke haɗa wannan rahoton, hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna ba ta ce uffan ba game da sabon harin Igabi.
A wani labarin na daban kuma A karon farko, Mace yar shekara 38 ta bayyana kudurinta na zama shugaban kasa a 2023
A tarihin Najeriya ba'a taba samun mace da ta zama shugaban ƙasa ba tun bayan samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960
Wata matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana sha'awarta na maye gurbin shugaba Buhari a babban zaben 2023 dake tafe.
Asali: Legit.ng