Bangaren Sheikh Gumi ya maida martani kan kashe shugabannin yan bindiga a Zamfara
- Sansanin Sheikh Ahmad Gumi, ya nemi dakarun sojin sama su bada hujjoji kan ikirarinsu na kashe shugabannin yan bindiga
- Sashin malamin wanda ya yi kaurin suna wajen bukatar ayi sulhu, yace kashe shugaban yan bindiga daya ba abin murna ba ne
- Daya daga cikin yan tawagar Gumi, Tukur Mamu, yace ko sojoji sun kashe ɗaya to wani mai hatsari fiye da shi zai bayyana
Yobe - Yayin da yan Najeriya ke murnan nasarar da sojiji suka samu a Zamfara na kashe shugabannin yan binidga, sansanin shahararren malamin nan, Sheikh Gumi, ya nuna tantama kan lamarin.
Bangaren Malamin, waɗan da ke ganin hanyar sulhu ce kaɗai mafita, ya yi kira ga rundunar soji ta tabbatar da ikirarinta ta hanyar bayyana hujjoji.
Jaridar Vangaurd ta rahoto ɗaya daga cikin mambobin bangaren Gumi, Ɗan Iyan Fika a jihar Yobe, Alhaji Tukur Mamu, na cewa ya kamata mutane su tambayi kansu ina shaidar kashe yan bindigan.
A wata hira da Trubune ta rahoto, Tukur Mamu, yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Tambayar da ya kamata mu yi wa kan mu shi ne, rahoton da suke yaɗawa cewa sun yi ruwan bama-bamai a sasanin yan bindiga, shin akwai wata kwakkwaran sheda a ƙasa?"
"Akwai wani daji da muka je a jihar Neja, baki ɗayansa an yi fata-fata da shi da ruwan bama-bamai, amma kwata-kwata dajin ba shi da alaƙa da maɓoyar yan bindiga."
"Daga karshe ma yan bindigan ne suka nuna mana wani rami guda biyu cike da gawarwakin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, waɗan da suka mutu sakamakon harin bama-baman sojojin."
Shin ya yan bindigan ke yi don tsira?
Haka nan kuma ya kara da cewa yan bindigan sun shaida musu cewa da zaran sun ji ƙaran zuwan jirgin yakin sojoji sai su gudu wani wuri su boye.
"Sun faɗa mana cewa da sun ji karar zuwan jirgi, sai su tsere zuwa kogonni su buya. Idan ma sun samu nasarar kashe wasu, to kananan yara ne ko mata ko kuma shanu."
Meye amfanin kashe shugabannin yan bindiga?
Kazalika Dan Iyan Fika yace meye amfanin kashe jagororin yan bindiga matukar hakan zai kara haifar da wasu da suka fi na baya hatsari.
"Naji ana ta murnan kashe wasu shugabannin yan bindiga. Alal misali, yau an kashe wani shugaban yan bindiga kuma wani sabo ya bayyana, meye amfanin hakan?"
"Misali kun kashe Dogo Gide, wani da ya fishi hatsari ya bayyana. Lokacin da suka kashe Buharin Daji, sai kuma Turji ya bullo, menene nasara anan?"
"Don haka babu wani abun murna anan, a wurin mu idan ma zamu yi murna to sai lokacin da sojoji suka kashe yan bindiga baki ɗaya, kuma ba za su iya ba."
A wani labarin kuma Gwamna Lalong ya lashi takobin aika duk dan bindigan da ak akam zuwa Lahira
A yan kwanakin, nan jihar Filato ta fara fama da yawaitar hare-haren yan bindiga dake sace mutane domin neman kudin fansa.
Gwamna jihar, Simon Lalong, ya gargaɗi duk masu hannu a irin wannan harin su gaggauta barin jihar Filato baki ɗaya ko kuma su fuskanci hukuncin kisa.
Asali: Legit.ng