Tuna baya: Buhari ya kasa cika alkawurransa saboda bashi da mukarrabai nagari, Bashir Tofa
- Bashir Tofa a wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da shi a 2020 ya ce shugaban kasa ya kasa cika alkawuran da ya dauka
- A cewarsa, hakan ya biyo bayan yadda ya rasa mutanen da ya dace da zasu tallafa masa su yi aiki tare don cika alkawurran
- A cewarsa, matsawar mutum ya rasa mataimaka na kwarai, dole ya yi hakuri da caccakar jama’a wadanda zasu dinga kushe shi
Kano - Alhaji Bashir Othman Tofa wanda ya tsaya takarar shugaban kasa karkashin NRC a zaben da aka yi ranar 12 ga watan Yunin 1993 wanda aka rushe sakamakon zaben ya tattauna da Daily Trust a watan Maris din 2020.
Sun yi maganganu akan rashin tsaron da Najeriya take fama da su da kuma batun rashin cika alkawuran da shugaba Buhari ya yi.
Kamar yadda Tofa yace:
“Zan maimaita abinda na dade ina fadi. Shugaban kasa ya rasa mataimakan da suka dace su tallafa masa ya tabbatar da alkawuran da ya dauka.
“Idan babu mataimakan da suka dace, zai ci gaba da shan caccaka. Na yarda da cewa yana da kudiri mai kyau akan kasar nan kuma idan ya sa hannu akan wasu ayyuka, kawai yana yarda da cewa an aiwatar da su ne.
“Matsalar shi ne, ta yuwu ba ya samun damar bin ayyukan don ya tabbatar da yin su kuma maganar gaskiya ya kamata ya yarda da gaskiya.”
Tofa ya yi wa Buhari fatan Ubangiji ya ba shi lafiya kuma ya bude masa idanunsa don ya gane gaskiya kuma ya yi aiki a kan ta. Saboda lokaci kullum kara tafiya ya ke yi.
Sun tattauna da shi akan matsalar rashin tsaron da kullum take kara hauhawa a yankin arewa maso gabas musamman matsalar Boko Haram da ‘yan bindiga.
A cewarsa, ana cikin mummunan yanayi don a shekarun baya idan da za a ce hakan za ta faru ko SSS za su ce ba zai yuwu ba.
Don haka ya ce, ya kamata gwamnati ta nemi sanin dalilin da yasa suke aiwatar da wadannan munanan ayyukan don su san hanyar da zasu bullo wa lamarin.
Ya ce ana kiran mutane ‘yan ta’adda, ‘yan shaye-sheye, barayi da sauransu ba tare da sanin dalilin da yasa su ke ta’addancin ba, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa, sanin hakan ne zai taimaka wurin yakar duk wasu tashin hankali da rashin tsaro tare da kawo zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.
Bashir Tofa, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 1993, Ya Rasu
A wani labari na daban, Alhaji Bashir Tofa, ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban kasa a zaben 1993, wanda ake yi wa kallon zabe mafi adalci a Najeriya, ya rasu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da ya ke tabbatar da rasuwarsa, dan uwan marigayin ya ce, "Alhaji Bashir Tofa ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya."
Asali: Legit.ng