Zamfara: Abin da yasa shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, ya sako mutum 52 da ke hannunsa

Zamfara: Abin da yasa shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, ya sako mutum 52 da ke hannunsa

  • An ci gaba da samun hujjoji akan dalilin da yasa shu’umin shugaban ‘yan bindigan jihar Zamfara, Bello Turji ya saki wasu mutane 52 da suka dade a hannunsa
  • Sakin jama’an kamar yadda manema labarai su ka gano ta yuwu yana da alaka da tattaunawar bayan fagen da shugabannin jihar Zamfara su ka yi da Turji
  • An samu rahotanni akan yadda wasu daga cikin wadanda Turji ya saki su ka zarce watanni biyu a hannun yaransa kuma yawanci mata ne wadanda ‘yan uwansu su ka gaza tara makudan kudaden fansa

Jihar Zamfara - Ana ta ci gaba da tattaro bayanai akan dalilin da yasa gawurtaccen dan bindigan jihar, Bello Turji ya saki mutane 52 ba tare da amsar ko sisi ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan neman sulhu, shugaban 'yan bindiga,Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa sakin yana da alaka da wata tattaunawar sirri da Turji ya yi da shugabannin jihar Zamfara.

Zamfara: Abin da yasa shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, ya sako mutum 52 da ke hannunsa
Dalilin da yasa shugaban ‘yan bindigan Zamfara, Bello Turji, ya saki mutane 52 da ke hannunsa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Wata takarda wacce aka ruwaito tun farkon watan Disamba ta nuna yadda wasu wakilai daga garin Shinkafi su ka kai wa Turji ziyara don su tattauna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Turji ya yi kaurin suna akan halaka rayuka da garkuwa da mutane musamman a yankin Shinkafi, Sabon Birni da karamar hukumar Isa da ke jihar Zamfara da Sokoto.

Yawanci sun wuce watanni biyu a hannun ‘yan bindigan

An tattaro bayanai akan wadanda aka sakin kasancewar yawancinsu mata ne kuma yaran Turji da ke Shinkafi zuwa Isa, Isa zuwa Sabon Birni da kuma hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi ke kulawa da su.

Kamar yadda majiyar ta shaida wa Daily Trust ta wayar Salula:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai wa fasinjoji hari a jirgin ruwa, sun yi musu fashi sun kuma sace jirgin

“Yawancinsu sun wuce watanni biyu a hannun ‘yan bindigan kuma an saki wasu ne bayan amsar kudaden fansa. Wadanda kuma ‘yan uwansu su ka kasa bayar da makudan kudaden su ne su ka kai wannan lokacin a hannunsu har sai wannan karon da Allah ya cece su.
“An ajiyesu a sansanin Turji wadanda yaransa ne suke kulawa da su ciki har da wani Danbokolo. Wani mazaunin yankin ya bayyana yadda su ka ga an ajiye wasu a sansanin Danbokolo lokacin su na yawo a ababen hawa.”

An wuce dasu Gusau don a hada su da ‘yan uwansu

A lokacin rubuta wannan rahoton, an shigar dasu ababen hawa kuma ana kokarin wucewa da su Gusau inda za a tattauna da su sannan a hada su da ‘yan uwansu.

Majiyoyi sun ce ta yuwu an takura wa Turji ne sakamakon wannan luguden wutar da sojoji su ke kai wa har ya kai ga halaka ‘yan uwansa da yaransa.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

A watan da ya gabata Turji ya tura wa masarautar Shinkafi wasika inda ya nuna cewa a shirye su ke da su zubar da makamansa don rungumar zaman lafiya.

Majiyoyin sun shaida cewa tattaunawar da su ka yi da Turji ne ya sa ya saki mutanen da ya yi garkuwa da su.

Akwai wadanda ke zargin ya na shirin sauya sansani ne

Sai dai wasu mazaunan sun ce akwai yuwuwar Turji ya na shirin barin yankin ne gaba daya matsawar ba zubar da makamansa ya yi ba.

Wani malamin tarihi a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, Dr Murtala Ahmed Rufa’i ya yi kira ga gwamnati akan ta kula da zama da Turji kuma su zama masu taka tsan-tsan.

A cewarsa duk da dai Turji ya yi kaurin suna saboda laifukan da ya tafka a baya, babu wata matsala akan zama don tattaunawa da shi amma daga karshe a tabbatar an yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata.

Kara karanta wannan

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

Dr Rufa’i ya bayar da misali da yadda aka dade ana zaman sasanci da ‘yan ta’adda amma babu wata nasarar da ake ci.

“Abinda ya fi muhimmanci shi ne ya kamata jami’an tsaro musamman sojoji su gane mutanen nan da salonsu da kuma hanyoyin da za a bullo musu don kawo karshen su,” a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164