Daga ƙarshe: Gwamnan APC ya bayyana sunayen masu ɗaukan nauyin ta'addanci a jiharsa

Daga ƙarshe: Gwamnan APC ya bayyana sunayen masu ɗaukan nauyin ta'addanci a jiharsa

  • Gwamnatin Jihar Imo ta ambacci Sanata Rochas Okorocha mai wakiltan Imo ta yamma da surukinsa, Uche Nwosu cikin wadanda ke daukan nauyin ayyukan ta'addanci a jihar
  • Gwamnatin ta ce wasu da jami'an tsaro suka kama kan zargin aikata laifukan ta'addanci a jihar sun ambaci sunayen Rochas da Nwosu a matsayin masu daukan nauyin ta'addanci
  • Gwamnatin na Imo kuma ta ce a maimakon Okorocha da Uche su wanke kansu daga zargin, sun bige da zuwa kafafen watsa labarai suna yi wa jami'an tsaro sharri da karya

Imo - Gwamnatin Jihar Imo ta ambaci sunan Rochas Okorocha, sanata mai wakiltan Imo ta yamma, da Uche Nwosu, tsohon dan takarar gwamna na jam'iyyar Action Alliance, AA, a matsayin masu daukan nauyin masu garkuwa da 'yan bindiga a jihar.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

Oguwike Nwachuku, babban sakataren watsa labarai na Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, The Cable ta ruwaito.

Daga ƙarshe: Gwamnan APC ya bayyana sunayen masu ɗaukan nauyin ta'addanci a jiharsa
Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana sunayen masu ɗaukan nauyin ta'addanci a jiharsa. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Nwachukwu ya ce gwamnan zai bayyana sunayen masu daukan nauyin yan bindiga da masu garkuwa da mutane yayin taron masu ruwa da tsaki a jihar a ranar Talata, rahoton The Cable.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Babu shakka, wadanda ake zargi da ke hannun jami'an tsaro sun ambaci sunayen Okorocha da Nwosu a matsayin masu daukan nauyin garkuwa da mutane da yan bindiga a jihar Imo, suna amfani da alakarsu da tsaffin 'yan tada kayan baya suna aikata laifuka."
"A maimakon su wanke kansu daga zargin, sun bige da amfani da hanyoyin bayyana da boye don yi wa rundunar 'yan sanda sharri, wacce ta kama Uche Nwosu bisa ka'ida. Suna kuma kokarin bata sunan jami'an yan sandan da ke tsare gwamnan Jihar Imo.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnan APC zai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Jiharsa

"Ana kyautata zaton Gwamna Hope Uzodinma zai yi amfani da taron masu ruwa da tsakin don fallasa sunayen wadanda ke daukan nauyin laifuka da tada zaune tsaye a jihar Imo. Hakan yasa mazauna Imo sun zuba ido domin sanin sunayen wadanda ke hana jihar cigaba. Hakan yasa Rochas da Uche suke ta bilayi a kafafen watsa labarai wadda hakan na karfafa cewa akwai hannunsu."

Gwamnan ya karyata cewa an kama babban jami'in tsaronsa

Har ila yau, gwamnan na Imo ya ce ikirarin da su Okorocha su kayi na cewa an kama babban jami'in tsaronsa mai suna Shaba karya ne, domin Shaba ba sunan mai tsaron gwamna bane.

Bugu da kari, babu wani jami'in tsaro a tawagar gwamna da ba a san inda ya ke ba a halin yanzu. Don haka labarin na kanzon kurege ne da aka kirkira domin wofintar da tunanin al'ummar gari.

'Yan sanda sun kama surukin Okorocha a cikin coci a Imo

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

A wani labarin, kun ji cewa an shiga rudani a cocin St Peters da ke Eziama Obire a karamar hukumar Nkwere na jihar Omo, a ranar Lahadi, a lokacin da aka kama Uche Nwosu, surukin Sanata Rochas Okorocha.

Yayin yadda aka kama shi ya janyo mutane suke tunanin kama sace Nwosu aka yi. A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ga mutane da bindiga suna awon gaba da Nwosu, a lokacin da ya hallarci addu'ar da ake yi bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164