Rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da matasan Akwa Ibom, mutum 3 sun rasa rayyukansu

Rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da matasan Akwa Ibom, mutum 3 sun rasa rayyukansu

  • Riciki ya barke a Afaha Oku, garin Ikpa da ke karkashin karamar hukumar Uyo a cikin jihar Akwa Ibom wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ‘yan jari-bola biyu
  • An samu bayanai akan yadda matasan Akwa Ibom su ka yi wa Hausawan kisan ature a matsayin ramako akan halaka wani dan yankinsu, Anietie da su ka yi
  • Wani mazaunin yankin wanda bai bukaci a bayyana sunansa ba, ya labarta yadda lamarin ya auku, inda ya ce da misalin karfe 9 na safiyar 2 ga watan Janairun 2020 rigimar ta hautsine

Akwa Ibom - Wata rigama ta barke a Afaha Oku da ke garin Ikpa a karkashin karamar hukumar Uyo cikin jihar wanda ya yi sanadin mutuwar wasu ‘yan jari bola guda biyu, The Punch ta ruwaito.

An tattaro bayanai akan yadda jama’a su ka taru wurin yi musu kisan ature saboda zarginsu da zama sanadiyyar mutuwar wani dan jihar, Anietie.

Kara karanta wannan

Dan kasuwa ya daba wa matarsa wuka har lahira bayan ya dirka mata saki a Adamawa

Rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da matasan Akwa Ibom, mutum 3 sun rasa rayyukansu
Mutane 3 sun rasa rayukansu, bayan rikici ya hada matasan Akwa Ibom da wasu Hausawa. Hoto: Daily Trust
Asali: Depositphotos

Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci The Punch ta sakaya sunansa ya ce lamarin ya auku ne a ranar 2 ga watan Janairun 2022 da misalin karfe 9 na safe.

Tushen lamarin

A cewarsa:

“Farkon abinda ya faru shi ne matasan kauyen ne su ka banka wa wasu Hausawa biyu ‘yan jari bola wuta bayan kama su da laifin halaka wani dan asalin kauyen Afaha Oku, Anietie bayan wani rikici ya hada su.
“Anietie ya je amsar kayansa ne daga shagon wanki da safiyar Lahadi, sai dai yana hanyarsa ta komawa gida ya hadu da wasu Hausawa ‘yan jari bola dauke da wasu karafa da suka sace daga gidansu.
“An sanar da ni yadda ya tsayar dasu ya na tambayarsu abinda su ke yi a harabar gidan. Cikin fushi Hausawan su ka fara dukansa har sai da ya rasa inda kansa yake. Bayan dan’uwan Anietie ya hango yadda lamarin ya auku ne ya fara neman taimako.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Mutanen da su ka kai dauki ne su ka babbaka ‘yan jari bolan

A cewarsa mutane sun yi saurin isa wurin inda su ka yi ram da hausawan. Daga baya aka samu labarin mutuwar Anietie bayan wucewa da shi asibiti.

Cikin fushi jama’a su ka hankada Hausawan cikin kwata tare da banka musu wuta inda su ka kone kurmus har lahira.

Kwamshinan ‘yan sanda ya bayar da umarni akan bincike mai zurfi

Jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Odika MacDon ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace kwamishinan ‘yan sandan jihar, Andrew Amiengheme ya bayar da umarnin yin bincike akan lamarin.

Sai dai kakakin ‘yan sandan ya nuna rashin jin dadinsa akan kisan inda yace dama matasan sun kai ‘yan jari bolan gaban hukuma ba tare da daukar mataki da hannayensu ba.

MacDon ya bayyana yadda binciken da aka fara yi ya nuna cewa ‘yan jari bolan sun saci abubuwa a gidansu Anietie ne lokacin da mutane su ka wuce coci.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

Ya kara da cewa:

“Kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin yin bincike mai zurfi akan lamarin kuma ya hori jama’a da su guji daukar doka a hannunsu.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164