Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga
- Gwamnan jihar Kaduna, ya ce kamata ya yi a saka bama-bamai domin su kone dukkan dajika da 'yan ta'adda da suka addabi jama'a
- El-Rufai ya ce dole za a fuskanci babbar barna, amma hakan ne kadai zai sa a tseratar da mutane su dawo gidajensu tare da cigaba da ayyukan habaka tattalin arziki
- Dan siyasan ya ce za a iya sake dasa bishiyoyi amma a baya rashin kayan aiki da fasaha ga hukumomin tsaro ne yasa aka dauka dogon lokaci ba a ga bayansu ba
Kaduna - Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce jami'an tsaro su sakarwa dajika bama-bamai domin ganin bayan 'yan bindiga.
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin zantawa da Arise TV a ranar Litinin. El-Rufai ya alakanta dogon lokacin da aka dauka ba tare da gamawa da 'yan bindiga a arewa maso yamma ba da rashin kayan aiki a kasa.
Ya kara da cewa, zuba kudade a fannin tsaro, fasaha da siyan kayayyakin amfanin jami'an tsaro zai kawo karshen 'yan bindiga da gaggawa, TheCable ta ruwaito.
"Wadannan 'yan bindigan suna barna ne kusa da mu saboda dajikanmu ne wurin buyarsu. Wannan babbar matsala ce. Hukumomin tsaro suna yin iyakar kokarinsu amma kuma abun ya yi musu yawa," yace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Abun da ke bayyane shi ne babu kayan aiki a kasa domin shawo kan kalubalen tsaron da muke fuskanta kuma wadannan kalubalen tsaron sun bazu kuma babu wani sashin kasar nan da zai ce bashi da matsalar tsaro.
“Mu kara kayan aiki, fasaha da karin zuba kudade wurin siyan makamai tare da kawar da su gaba daya.
"A koda yasuhe ni tunani na shi ne, a dasa bama-bamai a dajika mu kone su; za mu iya dasa wasu bishiyoyi. Mun dasa bama-bamai kwance a dajikan, su tashi da su duka. Za a samu barna sosai amma gara a batar da su duka kuma mutane su dawo yankunansu, su koma noma da kiwo tare da farfado da tattalin arziki."
Zamfara: Yadda luguden jiragen NAF ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga da wasu
A wani labari na daban, luguden wutar jiragen saman sojin sama na Najeriya a sa'o'in farko na ranar Asabar ya yi ajalin rayukan shugabannin 'yan bindiga biyu da wasu miyagun 'yan ta'adda da ke addabar jama'a a karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.
Daily Trust a ranar Lahadi ta tattaro cewa, gagararren dan bindiga, Alhaji Auta, ya sheka lahira bayan bam din da jirgin sojoji ya wurga ya tashi da shi yayin da ya ke kan babur tare da shanunsa daga sansaninsu.
Farmakin ya lamushe rayukan wasu 'yan kungiyarsa da ke kusa da sansani da kuma wadanda ke yankin, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng