Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa

Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa

  • Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna
  • Ya bayyana haka ne a gidan radiyon Invicta, inda ya bayyana kadan daga cikin manufofin da yake son cimmawa
  • Hakazalika, Sani ya kuma bayyana cewa, shi ba zai rabawa talakawa kudi ba, amma zai roke su su zabe shi don kawo ci gaba

Kaduna - Sanata Shehu Sani ya nuna sha’awarsa ta shiga jerin 'yan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 mai zuwa a badi, Daily Trust ta rahoto.

Tsohon sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan rediyon Invicta FM.

Sanata Shehu Sani kan batun tsayawa takarar gwamna
Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa | Hoto: Sehu Sani
Asali: Facebook

A cikin wani rufa-rufa da ya yi kan Gwamna Nasir El-Rufai, ya ce duk wanda ke zagi da cin mutuncin jama’a bai cancanci ya hau mulki ba saboda girmama dan Adam na da matukar muhimmanci a addini.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

Ya ce ya rage wa jam’iyyar PDP ta hada kan ‘ya’yanta don ganin sun kafa gwamnatin da za ta mutunta ra’ayin talakawa a Kaduna.

A kalaman Shehu Sani:

“Mun zauna da magoya bayana da masoya na kuma suna so in tsaya takarar gwamnan jihar Kaduna wanda zan yi don kawar da APC, in Allah Ya yarda; ya tsige zababben dan takarar gwamnan jihar sannan ya shiga gidan gwamnati inda za a rantsar da Kwamared a matsayin gwamnan da zai kawo sauye-sauye, wanda zai share duk wata kazantar da suka kawo jihar da sunan ci gaba.”
“Zan inganta tsaro. Wannan shi ne abin da magoya bayana suka so kuma na amince da su. Don haka zan tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP. Don haka ina kira ga al’ummar Kaduna da su ba ni goyon baya, su ba ni hadin kai.

Kara karanta wannan

Zamfara APC: Dan uwan Yari ya koma tsagin Matawalle, ya faɗi lokacin da Yari zai biyo bayansa

“Ina kuma rokon addu’o’insu; Ina bukatan addu'ar malaman addini, 'yan kasuwa, nakasassu, mata da matasa. Kun zabi Malam a matsayin Gwamna abin da ya rage a yanzu shi ne a samu Kwamared a matsayin gwamna don ganin bambancin da ke tsakaninmu.
“Dole ne ku ki zababbun 'yan takarar da suka rushe gidajenku. Ku tallafa mana don ganin yadda za mu kafa gwamnati mai mutunta ra’ayin talakawan jihar.”

Ya kara da cewa a matsayinsa na dan takara ba shi da kudin da zai raba wa wakilan da za su zabe shi, yana mai gargadin jama’a cewa siyasar kudi ita ce ta kawo kasar nan cikin mawuyacin hali a karkashin jam’iyya mai mulki.

Ya ce idan talaka ya yanke shawarar zabar shi da kudi ko ba tare da shi ba, zai yi nasara.

Ba wannan ne karon farko ba, gabanin zaben shekarar 2019, Shehu Sani a cikin shekarar 2018 ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna domin kalubalantar gwamna El-Rufai na jihar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

Jaridar The Guardian a shekarar 2018 ta tattaro yadda Sani yayi ikrarin barin jam'iyyar APC tare da bayyana aniyarsa ta shiga jerin 'yan takarar gwamna gadan-gadan.

Daga baya Shehu Sani ya bar jam'iyyar APC, amma duk da haka gwamna El-Rufai ne ya ci zaben gwamna a 2019 a Kaduna.

Zan nemi kujerar Malam El-Rufa'i a zaben 2023 karkashin PDP, Sanata Shehu Sani

A tun farko, tsohon sanatan yace zai nemi kujerar gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwan jam'iyyar PDP a babban zaben 2023.

BBC Hausa ta rahoto cewa tsohon dan majalisar dattijai ya jima da ficewa daga jam'iyyar PRP, wacce ya nemi zarcewa kujerar sanata a shekarar 2019 amma bai bayyana inda ya koma ba.

Sai dai a ranar Asabar da PDP ta gudanar da gangamin taron ta na kasa, an hangi Shehu Sani ya halarci taron, hakan ya tabbatar da ya koma jam'iyyar.

Kara karanta wannan

A kusan karon farko, rikakken ‘Dan adawa, Sule Lamido ya yabawa matakin da Buhari ya dauka

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.