Fusatattun matasa sun farmaki manyan sarakunan jihar Bauchi

Fusatattun matasa sun farmaki manyan sarakunan jihar Bauchi

  • Matasa a Bogoro da ke jihar Bauchi sun kona gidaje da sauran kayayyaki na miliyoyin naira a bikin cika shekaru 21 da mutuwar shugaban al'umman Sayawa, Baba Peter Gonto
  • An shirya taron ne domin karrama Gonto, mutum na farko da ya karbi addinin kiristanci a kasar Sayawa
  • Hakazalika matasan sun farmaki Sarakunan Bauchi da Dass a hanyarsu ta zuwa Bogoro

Bauchi - Fusatattun matasa a karamar hukumar Bogoro da ke jihar Bauchi sun kona gidaje da sauran kayayyaki na miliyoyin naira lokacin bikin cika shekaru 21 da mutuwar shugaban Sayawa, Baba Peter Gonto.

Gonto ya kasance mutum na farko da ya karbi addinin kiristanci a kasar Sayawa, wanda ya haifar da rabuwar kai a tsakanin mutanen Sayawa a kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 14, an cigaba da shari'ar wawurar kudaden da tsohon gwamnan arewa ya yi

Matasan sun kai mamaya ainahin wajen taron a makarantar sakandaren jeka-ka-dawo na gwamnati, Bogoro, inda suka cinnawa kayayyakin da aka yi amfani da su wajen taron wuta bayan kammala taron.

Fusatattun matasa sun farmaki manyan sarakunan jihar Bauchi
Fusatattun matasa sun farmaki manyan sarakunan jihar Bauchi Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

Sun fara kai farmaki ga ayarin motocin sarakunan Bauchi da Dass a hanyarsu ta zuwa Bogoro sannan suka bata motar sarkin Dass da sauran motocin ayarinsa, inda suka tursasa su juyawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed, wanda ake sa ran zai zama bako na musamman a taron, bai samu halartan taron ba saboda dalili na tsaro, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Manema labarai basu samu shiga Bagoro ba yayin da matasan suka rufe dukka hanyoyin da zai sada mutum da garin sannan suka tursasa su juyawa bayan samun labarin rikici na wakana a mararrabar Bogoro.

Punch ta kuma rahoto cewa matasan sun toshe hanyoyin shiga Bogoro daga Gwarangah da Mwari yayin da aka kuma kona wasu gidaje a Bogoro baya ga wadanda aka kona a garin Tafawa Balewa a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

2023: Babban faston Najeriya ya bayyana wanda zai gaji Buhari

An tattaro cewa sun yi zanga-zangar ne saboda wadanda suka shirya taron sun ki sanya wasu manyan ‘yayan yankin a tsare-tsaren taron.

An tattaro cewa tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya rubuta wata wasika zuwa ga Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba, don sanar masa da yiwuwar barkewar rashin zaman lafiya a yankin.

Dogara, wanda ya kasance mamba mai wakiltan Bagoro/Dass/Tafawa Balewa ya bukaci wadanda suka shirya taron da su sanya hannu a yarjejeniyar daukar alhakin duk abun da zai biyo baya.

A halin da ake ciki, kwamishinan yan sandan jihar, Umar Mamman Sanda, ya yi umurnin bincike cikin lamarin karya doka da oda a yankunan Bogoro da Tafawa Balewa.

Kakakin yan sandan jihar, Wakili Ahmed ya ce kwamishinan ya roki jama’a da su kwantar da hankalinsu kuma kafa su dauki doka a hannunsu.

An gudanar da taron kade-kaden da ya gabata a ranar Alhamis a Cocin dake kauyen Mwari na marigayi Baba Peter Gonto wanda ya kunshi fitattun mawakan bishara karkashin jagorancin Panam Percy Paul.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

Bidiyon Sarkin Bauchi yana rera wakar yabo yayin da ya karbi bakuncin Kiristoci a fadarsa

A wani labarin, mun kawo a baya cewa mai martaba sarkin Bauchi ya karbi bakuncin wasu mabiya addinin Kiristanci a fadarsa a yayin bikin kirsimeti.

A yayin taron, sarkin wanda ya kasance Musulmi, ya yi wa kiristocin jawabi a kan gudanar da rayuwa mai kyau wanda za a yi koyi da shi.

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa a yayin taron, basaraken wanda ke zaune a kan kujerarsa ta mulki ya kuma rera wakar 'Annabi Isah na nan dawowa ba da jimawa ba'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng