Kudi $36bn nike bukata in dinke Najeriya da layin dogo, Rotimi Amaechi
- Ministan Sufuri ya bayyana cewa zai so ya samu kudi don hada Najeriya gaba daya da layin dogo
- Gwamnatin Buhari ta kammala ginin layin dogon Abuja-Kaduna, Legas-Ibadan, da kuma Itakpe-Warri
- Ministan ya ce nan da karshen shekarar 2022 za'a kammala hada Kano da Kaduna
Abuja - Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa $36bn kadai yake bukata ya dinke Najeriya gaba daya da layin dogo.
Amaechi ya bayyana hakan ne da safiyar Juma'a, 31 ga Disamba, a shirin 'Good Morning Nigeria' na tashar NTA.
A cewarsa, ginin layin dogo aiki ne mai lakume kudi sosai shi yasa kamfanoni masu zaman kansu ba zasu iya zuba kudi ba.
Ya ce dalilin da ya sa Gwamnatin Buhari ke karban basussuka don yin aikin shine an samu dukiyoyin da aka mika matsayin jingina.
Yayinda aka tambayesa shin meyasa ba a hada Abuja da Lokoja, Amaechi yace:
"Da muna da kudi, zan so ace ni ne Ministan da ya dinke Najeriya gaba daya. Da $36bn za'a hada duka."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Layin dogon Itapke zuwa Abuja $3.09bn ne. Da muna da wannan, gobe da safe zamu fara."
Nan da Disamba 2022 za'a kammala layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi
Amaechi ya bayyana cewa nan da karshen sabuwar shekarar da muke shirin shiga za'a fara amfani da layin dogon Kano zuwa Kaduna.
Ministan ya bayyana hakan ne a jihar Kano yayinda ya kai ziyarar ganin ido kan yadda aikin ke gudana, rahoton TheNation.
Amaechi ya kara da cewa Gwamnatin tarayya kawo yanzu ta zuba $400million wannan aiki kuma za'a kammala a kaddamar kafin wa'adin Shugaba Buhari ya kare a ofis.
Ya kara da cewa yan majalisar zartaswa sun sauya tsarin da aka yi na kashe $1.2billion kan aikin daga farko har karshe.
Asali: Legit.ng