‘Yan sanda sun kai samame sansanin ‘yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutum 9
- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kai samame sansanin Isiya, wani gawurtaccen dan bindiga a dajin Sabon Birni da ke karamar Igabi ta jihar Kaduna
- Jami'an rundunar sun kuma ceto wasu mutane tara da aka yi garkuwa da su domin kudin fansa
- Wannan nasarar ya samu ne a ranar Juma'a, 31 ga watan Disamba wanda ya yi daidai da jajiberin sabuwar shekara
Kaduna - Jami’an ‘yan sanda sun kai samame sansanin ‘yan bindiga mallakar wani Isiya, gawurtaccen dan bindiga a dajin Sabon Birni da ke karamar Igabi ta jihar Kaduna.
Rundunar ta ce an kashe dan fashi daya sannan aka kama wasu biyu a yayin aikin da ya gudana a ranar Juma’a, 31 ga watan Disamba, Daily Trust ta rahoto.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, rahoton Vanguard.
A cewarsa, jami’an rundunar jihar tare da hadin gwiwar sashin leken asiri na hedkwatar rundunar, Abuja da wasu yan banga ne suka aiwatar da aikin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma ce Jami’an sun ceto mutane tara da aka yi garkuwa da su a lokacin da suka farma sansanin bayan samun bayan sirri cewa ana rike da su don kudin fansa a dajin.
Ya ce:
“An aiwatar da aikin cikin kula da nasara wanda ya kai ga kashe dan fashi daya, yayin da wasu da dama suka tsere da harbin bindiga.
“An kama mutum biyu masu suna Rabe Bushe da Badamasi Usman kuma suna tsare don ci gaba da bincike."
A halin da ake ciki, tuni aka sada mutane takwas cikin tara da aka ceto da yan uwansu bayan an masu gwaje-gwaje a asibitin yan sanda.
Ya ce an gaggauta kai dayan asibitin koyarwa na Barau Dikko Kaduna bayan ya samu raunuka daga harbin bindiga.
Kwamishinan yan sandan Kaduna, CP Mudassiru Abdullahi psc, ya yaba da jajircewar Jami’an.
Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara
A gefe guda, mun ji cewa a kalla mutane 12, ciki harda mata 10 ne aka yi garkuwa da su lokacin da yan bindiga suka kai hari kauyen Kerawa da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Juma’a, 31 ga watan Disamba.
Wani jagoran matasa a garin, Jamil Kerawa, ya tabbatar da harin, yana mai cewa yan bindigar sun ci karensu ne ba babbaka.
Asali: Legit.ng