Filin Fatawar Juma'a: Wanda ya auri mace kafin ta gama Idda, babu aure tsakaninsu har Abada
Kamar yadda muka saba ranar Juma'a, Legit Hausa kan kawo fatawowi da tsokacin Malamai kan wasu mas'alolin addini da suke shigewa mutane kuma ake bukatan bayani ta ilmi a kai.
Wannan karo mun kawo muku amsar wata tambaya da aka yiwa Sheik Dr. Jamilu Yusuf Zarewa, Malami a tsangayar nazarin addinin Musulunci dake Jami'ar Ahmadu Bello dake Kaduna (ABU Zaria)
Tambaya:
Wata ce take tare da mijin ta na farko, sai wani ya taimaka mata har ta fito daga gidan, kuma ya aure ta kafin iddar ta ta cika.
Toh tana zaune sai ta ji a Sunna TV ana maganar wannan matsalar, sai ta sanar da mijin, ta nemi su rabu, sai ya ba ta Qur'ani ta rantse cewar idan ta kammala iddah, za ta aure shi.
Menene hukuncin aurenta da mutumin nan, kuma menene hukuncin rantsuwarta ?, domin yanzu tana so jibin nan a daura mata aure da wani mutumin daban.
Allah Shi ba da lada.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amsar Malam:
Wa alaikum assalam, Auren da suka yi batacce ne, saboda Allah ya hana Aure a cikin idda a cikin suratul Bakara aya (235), sannan
a Mazhabar Malikiyya babu Aure a tsakaninsu da wancan mijin har abada tun da ya aureta a cikin idda, saboda Ka'idar:
من تعجل شيئا قبل أوانه عوقب بحرمانه
Duk Wanda ya gaggauta abu kafin lokacinsa za'a yi masa ukuba, ta hanyar haramta masa abin.
Idan ta yi kaffara Shikenan ta warware rantsuwarta, Annabi (SAW) yana cewa "Idan ka yi rantsuwa ba za ka yi abu ba, sai ka ga aikata abin ya fi alkairi to ka yi kaffara sai ka aikata abin da ya fi alkairi"
Ya wajaba su gaggauta tuba saboda sun yi Aure a cikin Aure, Allah ya kare mu daga karkacewa da kuma son zuciya.
Allah ne mafi sani
Asali: Legit.ng