Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai sabon hari jihar Kaduna, inda suka sace wasu mata a wani yankin jihar
  • An sace matan ne washe garin sabuwar shekarar 2022 da za a shiga gobe, lamarin da ya haifar firgici a yankin
  • Wani mazaunin yankin ya bayyana yadda 'yan ta'addan suka tafka irin barnar da suke so kuma suka yi tafiyarsu

Kaduna - Akalla mutane 12, ciki harda mata 10 ne aka yi garkuwa da su lokacin da yan bindiga suka kai hari kauyen Kerawa da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Juma’a, 31 ga watan Disamba.

Harin 'yan bindiga a jihar Kaduna
Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin Kirsimeti | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani jagoran matasa a garin, Jamil Kerawa, ya tabbatar da harin, yana mai cewa yan bindigar sun ci karensu ne ba babbaka.

Ya ce:

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

“Sun yi garkuwa da mutane 12, maza biyu da mata 10 bayan sun kashe mutum daya. Sun kuma raunata wani inda aka kwashe shi zuwa asibiti a Zaria. Muna bukatar agaji a Kerawa saboda Allah ne kadai ke kare mu.”

Ya roki gwamnatin jihar da ta zuba Jami’an tsaro a yankin, inda ya koka da karuwar hare-hare.

Daily Trust ta rahoto cewa kauyukan da ke kewaye irin su Hauin Dam, Rago, Unguwar Salahu da Zariyawa duk sun fuskanci hare-haren yan bindiga a baya-bayan nan.

Wani mazaunin yankin mai suna Jafaru ya ce dan uwansa na jini da dan kawunsa na daga cikin wadanda aka sace.

Ya ce garin gaba daya na cikin rudani.

Sai dai kuma babu wani bayani a hukumance daga gwamnatin jihar da rundunar yan sanda amma Kakakin yan sandan ya yi alkawarin yin tsokaci bayan samun karin bayani.

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun hallaka mutane sun sace mata 33

A wani labarin, 'yan bindiga sun tsinkayi yankin Mareri da ke babban birnin jihar Zamfara a ranar Juma'a kuma sun sace mata da diyar wani lakcaran kwalejin ilimi.

An gano cewa, sun kwashi dukiya daga gidan malamin mai suna Dr Abdulrazak Muazu, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Ba a tabbatar da cewa Muazu ya na gida ko ba ya nan ba lokacin da masu farmakin suka shiga gidansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng