Mota ta ƙwace wa 'yan sanda sun banke wani abokin aikinsu ɗan sanda a babur ya mutu
- Wasu yan sanda su takwas a cikin mota sun banke wani abokin aikinsu da ke kan babur bayan motarsu ta samu matsala
- Dan sandan da ke kan babur da suka banke ya riga mu gidan gaskiya bayan an garzaya da shi asibiti saboda raunin da ya yi
- Sauran yan sandan takwas da ke cikin motan sun jikkata sannan suna asibiti ana musu magani kamar yadda kakakin yan sanda ya sanar
Jihar Ekiti - Wani jami'in dan sanda da ba a bayyana sunansa ba ya riga mu gidan gaskiya a ranar Talata bayan motar yan sanda ta buge shi yayin da ya ke kan babur a jihar Ekiti, rahoton Daily Trust.
Jami'an yan sanda masu amsa kirar gaggawa na RRS guda takwas suma sun jikkata sakamakon hatsarin.

Source: Facebook
Mai magana da yawun yan sandan jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu, ya ce hatsarin ya faru ne yayin da jami'an ke amsa kirar neman kawo dauki da aka musu daga ofishin yan sanda na Ikole, Ekiti.
Ya ce motar sintirin yan sandan na cikin motocci uku da aka tura domin taimakawa yan sandan su kama wasu yan kungiyar asiri da ke adabar mutanen Ikole da kewaye.
Kalamansa:
"Yayin da suke hanyarsu na amsa kirar, motarsu ta samu matsala, ta sauka daga kan titi ta buge wani dan sanda da ke kan babur da ke hanyarsa na koma wa gida bayan ya tashi daga aiki.
"An garzaya da dan sandan zuwa asibiti domin masa magani amma likita ya tabbatar ya mutu yayin da sauran jami'an na RRS takwas da suka jikkata suna can asibitin ana musu magani."

Kara karanta wannan
Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda
Mai magana da yawun yan sandan ya mika sakon jeje na kwamishinan yan sanda, Tunde Mobayo, ga iyalan dan sandan da ya rasu.
Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira
A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.
An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.
Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.
Asali: Legit.ng
