Innalilahi: Wani magidanci ya kashe matarsa, Fatima, a Jigawa
- Wani magidanci, Yusuf Zubairu, ya halaka matarsa Fatima Hardo sakamakon cacar baki da ya shiga tsakaninsu a Jigawa
- Zubairu, mai shekaru 26 ya yi amfani da sanda ne ya rika dukar matarsa a jiki sannan ya buga mata a kai hakan yasa ta fadi nan take
- Har wa yau, Zubairu ya raunata wata makwabciyarsu mai suna Rabi wacce ta yi kokarin raba su fada a yayin da ta ga alamar zai halaka matarsa
Jihar Jigawa - Wani mutum mai suna Yusuf Zubairu, ya halaka matarsa mai suna Fatima Hardo, a karamar hukumar Sule Tankarkar a jihar Jigawa, Premium Times ta ruwaito.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar, Lawan Adam, ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba cewa lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Disamba a kauyen Baldi inda ma'auratan ke zama.

Source: Facebook
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani Bulama Muntari-Ubale, mai shekaru 65, ne ya kai wa yan sanda rahoton afkuwar lamarin da ya ce ya faru misalin karfe 11.30 na safe tsakanin Zubairu, 26 da matarsa, Fatima, 23 sakamakon rashin jituwa da ya shiga tsakaninsu.
Yadda abin ya faru
Mr Adam ya ce:
"A yayin da suke rikicin, Yusuf Zubairu (wanda aka fi sani da Sallau) ya yi amfani da sanda ya buga wa Fatima Hardo (marigayiyan) a kanta da sauran jiki.
"Da wata Rabi Lawan da ke zaune gida daya da su tazo raba fadan, Yusuf Zubairu ya mata mummunan rauni itama."
Yan sanda sun amsa kira cikin gaggawa
Ya ce bayan an shigar musu da korafin, an tura tawagar yan sanda zuwa wurin da abin ya faru cikin gaggawa sanan suka kai wadanda abin ya faru da su zuwa babban asibitin Gumel inda likita ya tabbatar ta mutu.

Kara karanta wannan
Yan Bindiga Sun Sake Tare Motocci a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari, Sun Bindige Mutane 6, Sun Sace Da Dama
Kakakin yan sandan ya ce yayin da Rabi (wace aka yi wa rauni) tana asibiti ana mata magani, an kama wanda ake zargin tare da kwato wasu abubuwa a hannunsa, rahoton Premium Times.
Adam ya kara da cewa ana cigaba da bincike.
An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona
A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.
Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.
Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.
Asali: Legit.ng
