Gwamnati Ta Gargaɗi 'Yan Najeriya Kan Shan Haɗe-Haɗen Magungunan Gargajiya

Gwamnati Ta Gargaɗi 'Yan Najeriya Kan Shan Haɗe-Haɗen Magungunan Gargajiya

  • Hukumar kula ingancin abinci da magunguna, NAFDAC, ta kara jan kunnen ‘yan Najeriya akan siyan magungunan gargajiya saboda rashin ajiyarsu da kyau
  • Darekta janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ya ja kunnen ‘yan Najeriya yayin da manema labarai su ka tattauna da shi a ranar Laraba a Legas
  • Shugaban NAFDAC din ya ce ba a san inda aka samo magungunan gargajiyan da ake yawo da su a tituna ba, kuma kwayoyin cuta su na tsirowa cikinsu bayan kwana 4 zuwa 5

Legas - Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci, NAFDAC ta ja wa ‘yan Najeriya kunne akan siyan magungunan gargajiya sakamakon rashin kula da su wurin ajiya, Daily Trust ta ruwaito.

Darekta janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta yi wannan jan kunnen yayin da wakilin NAN ta ke tattaunawa da shi a ranar Laraba a Legas.

Kara karanta wannan

Ku Kiyayi Shan Magungunan Ƙarfin Mazakuta, Za Su Iya Kashe Ku, Shugaban NAFDAC Ta Gargaɗi Maza

Gwamnati Ta Gargaɗi 'Yan Najeriya Kan Shan Haɗe-Haɗen Magungunan Gargajiya
FG ta gargadi 'yan Najeriya game da shan hade-haden magungunan gargajiya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shugabar NAFDAC din ta ce duk wani maganin da ake tallarsa a titi ko mota ba ya da inganci saboda rashin sanin inda aka samo shi.

Magungunan su na da hatsari ga lafiyar dan Adam

Kamar yadda tace:

“Musamman magungunan gargajiya na ruwa, kwayoyin cuta su na fara tsirowa a cikinsu bayan kwana hudu zuwa biyar kuma shan su zai iya zama hatsari ga rayuwar mutum.”

Adeyeye tace aikin hukumar NAFDAC ne tabbatar da ingancin duk wani abin da mutum zai ci ko ya sha saboda tabbatar da lafiyarsa.

Ta kara da cewa:

“Yawancin magungunan gargajiyanmu su na aiki amma akwai bukatar a yi bincike akan su don sanin yadda su ke aikin, da kuma yadda su ke lalacewa.”

Su na iya janyo wa mutum cutar daji

Kara karanta wannan

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

DG din ta ja kunnen jama’a akan amfani da magungunan saboda zasu iya janyo wa mutum cutar daji.

Ta ce maza da dama sun samu matsalar ciwon zuciya saboda amfani da magungunan kara karfin al’aura, wanda sanadin hakan suke halaka.

Hukumar za ta jajirce wurin hana amfani magunguna masu illa ga jikin jama’a

Adeyeye ta ce hukumar za ta ci gaba da amfani da salo na musamman don karfafa wa masu hadin magungunan asibiti guiwa don tabbatar da sun yi masu inganci da kuma nagarta.

Har ila yau, hukumar za ta jajirce wurin dakatar da hada abinci da magunguna masu kyau don kula da lafiyar ‘yan Najeriya.

Ku Kiyayi Shan Magungunan Ƙarfin Mazakuta, Za Su Iya Kashe Ku, Shugaban NAFDAC Ta Gargaɗi Maza

A wani labarin mai alaka da wannan, an gargadi maza su dena amfani da magungunan kara karfin mazakuta da aka fi sani da maganin karfin maza domin cigaba da amfani da su na iya janyo bugun zuciya ko mutuwar gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba

A sakon ta na Kirsimeti da sabon shekara ga ƴan Najeriya, Shugaban hukumar kula da magunguna da abinci, NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce mafi yawancin magungunan kara karfin mazan shigo da su ake yi ta haramtattun hanya.

Magungunan ƙara ƙarfin maza ana amfani da su ne domin ƙara daɗin kwanciya tsakanin masoya kamar yadda Leadership.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164