Yadda kare ya lamushe mazakutar mai gidansa bayan ya sha giya ya yi tatil a jejiberin kirsimeti

Yadda kare ya lamushe mazakutar mai gidansa bayan ya sha giya ya yi tatil a jejiberin kirsimeti

  • Yayin shagulgulan kirsimeti wani mai maganin gargajiya mai shekaru 60 mazaunin Calabar, Ani Ikoneto, ya shiga gagarumin tashin hankali bayan kare ya gatsi al’aurarsa
  • Mutumin mazaunin gida mai lamba 12 a layin Jebbs da ke kudancin Calabar ne kamar yadda makwabta su ka shaida, ya sha giya har yayi tatil ranar jajibarin kirismeti
  • Bayan ya shiga dakinsa ba tare da kulle kofa ba sai ya saki bayan gida, yayin da kare ya ji warin ya shiga, sai ya sami wuri ya zauna ya hau cin al’aurarsa, ya yi tunanin an bar nama ne a tsakiyan kashi

Jihar, Cross River - Bikin kirsimeti bai yi wa wani mai maganin gargajiya mai shekaru 60 a Calabar, Ani Ikoneto dadi ba, bayan kare ya gatsi al’aurarsa, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magidanci ɗan shekaru 80 ya kashe matarsa don ta fasa kwanciyar aure da shi bayan ya sha maganin ƙarfin maza

Mutumin wanda mazaunin gida mai lamba 12 ne a layin Jebbs a kudancin Calabar, kamar yadda makwabta suka shaida, sai da ya sha giya ya yi tatil ranar jajibarin kirsimeti.

Yadda kare ya lamushe mazakutar mai mai gidansa bayan ya sha giya ya yi tatil
Kare ya cinye mazakutar magidansa yayin da ya yi tatil da giya. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi bayan gida a kwance ne, hakan yasa kare ya yi tunanin an bar tsoka ne sai karen ya hau ci

Wani makwabciyarsa, Itoro ta shaida cewa:

“Bayan ya dawo gida duk munyi bacci amma akwai wadanda su ke waje sai ya shige daki ba tare da ya rufe kofa ba saboda yadda ya yi mankas da giya.
“Kare ya shiga dakinsa bayan ya ji warin bayan gidan da yayi, karen ya yi tunanin nama ne al’aurar mutumin sai ya ci wani bangare daga ciki a tsakiyar bayan gidan.”

Ihun da mutumin ya yi yasa makwabta su ka shiga dakinsa

Kara karanta wannan

"Yadda Gwamna mai-ci ya bada umarni a nemi ayi wa ‘Dan takarar Gwamna kusan zindir"

Vanguard ta rahoto yadda makwabciyar ta ce ihun da mutumin ya yi ne ya sa makwabta su ka yi gaggawar shiga dakinsa daga nan su ka ga aika-aikar da karen yayi.

Makwabtan sun ce sun yi tunanin ‘yan daba ne su ka kai masa farmaki amma bayan isarsu su ka ga bakin karen jina-jina yayin da bangaren al’aurar ya yi layar zana.

Sun fara wanke masa jiki kafin su zarce da shi asibiti

Itoro ta shaida yadda su ka fara gyara jikin mutumin saboda bayan gidan da yayi kaca-kaca a jikinsa sannan su ka iya wucewa da shi asibiti.

Sakamakon lokacin da su ka dauka kafin su kai shi asibiti jini ya dinga zuba sai mutuwa ya yi.

Dama mutumin shi kadai ya ke zama saboda yaransa mata duk sun yi aure kuma su na nesa da inda yake.

Sai washegari su ka wuce da shi kauyensu, Ikoneto don a birne shi.

Kara karanta wannan

Bai zo a littafi mai tsarki ba: Kirista ta caccaki masu bikin Kirsimeti

Wani mutum ya mutu wurin gasar cin abinci yayin bikin Kirsimeti a Uganda

A wani labarin, wani mutum mai shekaru 56 mai suna Sentekola Gad, ya shake kansa da abinci yayin gasar cin abinci a ranar Kirsimeti a kasar Uganda LIB ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sanda, Fred Enanga, ya ce Sentekola ya shiga gasar cin abinci ne da wani Salvan ya shirya a Kihiri, a yankin Kanungu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164