Yadda Shugaba Buhari Ya Ceto Najeriya Daga Rushewa bayan zaɓen 2015, Malami
- Malami yace shugaba Buhari ya yi abin da ba kasafai shugabanni ke iya yi ba cikin shekara ɗaya da hawansa karagar mulki
- Ministan yace Buhari ya samu ƙasar nan tana tangal-tangal, kuma ya ceto ta daga kifewar tattalin arziki, wanda ka iya watsa kasar
- A cewarsa Buhari ya samu nasara sosai ta bangaren tsaro fiye da gwamnatin da suka shude a baya
Abuja - Antoni Janar na ƙasar nan kuma ministan shari'a, Abubakar Malami SAN, yace shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ceci Najeriya daga rushewa cikin shekarar farko da kafa gwamnatinsa.
Daily trust ta rahoto Malami yace Buhari ya samu kasar nan a dai-dai lokacin da tattalin arziki ke gab da rushewa, wanda ka iya jawo watsewar ƙasar baki ɗaya.
Ministan, wanda ya faɗi haka a wani shirin gidan Radiyo a jihar Kano, yace kowane bangare na tatattalin arzikin Najeriya ya samu koma baya kafin zuwa shugaba Buhari.
Haka nan kuma Buhari ya ceci gwamnatocin jihohi daga matsi ta hanyar raba musu makudan kudaɗe a lokuta daban-daban.
Malami yace:
"Shugaban ƙasa ya yi wannan duk a cikin abin da bai kai shekara ɗaya ba; Ya ceci tattalin arziki daga mummunan faɗuwa, ba kasafai ake samun haka ba don ba kowane shugaba ne zai iya haka ba."
Ya ƙara da cewa shugaban bai tsaya iya nan ba, ya kirkiro abubuwa da dama da suka taimakawa yan Najeriya kamar tsarin N-Power da kuma tallafin COVID19.
A cewar ministan irin waɗan nan abubuwan da shugaba Buhari ya samar sun taimaka sosai wajen samar da aikin yi ga yan Najeriya da dama.
Ko me shugaban ya yi a bangaren tsaro?
Game da lamarin tsaro kuwa, Malami yace Buhari ya ɗauki tsaro da muhimmanci, inda ya ɗauki matakan hana yan ta'addan Boko Haram cigaba da kai muggan hare-hare.
Vanguard ta rahoto ministan yace:
"Kafin zuwan Buhari, akwai kalubale mai yawa a bangaren tsaro, amma yanzun mun samu nasarar hana kai hare-hare kamar na baya. An jima sosai kafin ka ji an kai hari kasuwa, ko wuraren ibada da sauran su."
Kazalika ministan yace jajircewan da hukumomin tsaro suka yi a arewa maso yamma, yasa yan bindiga suka fara neman yadda za'ai sulhu da gwamnati.
A wani labarin na daban kuma Hotunan yadda yan daba suka yi fata-fata da wurin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara
Wasu gungun yan daban siyasa sun farmaki filin da PDP ta shirya gudanar da zaɓen shugabanninta a matakin jiha a Zamfara.
Rahotannu sun bayyana cewa yan daban sun farfasa motoci, sun lalata runfunan da aka kafa, kuma sun yi kone-kone.
Asali: Legit.ng