Korona ta kara yawan bukatar zamanantar da harkar fasaha a Najeriya, Dr Pantami
- Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, ya ce Korona ta ba da damar habaka fasahar na zamani a Najeriya
- Pantami ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron gamayyar gudanar da mulki na Intanet na Afirka na 2021
- A cewarsa, kalubalen da cutar ta haifar ya tabbatar da an samu karuwar bukatar ayyukan Intanet a duk duniya
FCT, Abuja - Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Ministan Sadarwa na Najeriya, ya ce cutar Korona ta kara habaka bukatar yin la'akari da fasahar zamani ta yadda za a magance kalubalen da annobar ta haifar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ministan ya bayyana hakan ne a yayin taron gudanar da harkokin mulki na intanet na Afirka ta 2021 mai taken ‘Ci gaban sauye-sauyen fasahar zamani a Afirka ta fuskar rikici.’
Legit.ng ta tattaro cewa ya fadi haka ne a lokacin da yake magana ta bakin wani darakta a hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC), wanda kuma shine mai ba shi shawara kan harkokin fasaha, Sahalu Junaidu.
Pantami ya ce kalubalen da annobar ta haifar ya tabbatar da an samu karuwar bukatar ayyukan Intanet.
Yace:
"Cutar Korona ta kara habaka bukatar rungumar al'adun fasahar zamani. Don haka, a matsayinmu na ’yan Afirka, daya daga cikin hanyoyin da za mu iya mayar da martani ga kalubalen da annobar ta jefa mu ita ce hanzarta sauya tsarin mu na fasahar zamani."
Ministan ya ce, ya kamata a samo dabarun kawo sauyi na zamani ga Afirka kan muhimman ginshikai da dama, ciki har da fannin kirkire-kirkire na zamani da harkokin kasuwanci.
Ya kara da cewa sassa masu mahimmanci irin su kasuwancin intanet da sabis na kudi, gwamnatin dijital, ilimin dijital, kiwon lafiya na dijital, da aikin gona na dijital, suma suna jadada ginshikan sauyi.
An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro
A wani bangare na kokarin ganin an kiyaye dokar lafiya, hukumar babban birnin tarayya Abuja ta sanar da haramtawa wuraren shakatawa da bukukuwa da majami’u na addini da ke da mabiya sama da 50 yin taro.
Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 25 ga Disamba, ta ce an sanar da matakin ne sakamakon sake barkewar Korona
Hakazalika, gwamnati ta ce gazawar mazauna Abuja wajen daukar matakan kariya masu sauki abin damuwa ne ga lafiyar al'umma.
Gwamnatin, a cikin wata sanarwa da Sakataren, Sakateriyar Lafiya da Ayyukan Jama’a Dr. Abubakar Tafida ya fitar, ta yi kira ga mazauna Abuja da su dauki matakin kare kansu da ‘yan uwansu daga wannan annoba.
A wani labarin, Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya, NCDC ta tabbatar da bullar nau'in cutar korona na Omicron da ke firgita kasashen duniya. Hukumar ta ce an gano mutane biyu da ke dauke da nau'in cutar a halin yanzu.
Dr Ifedayo Adetifa, Direkta Janar na hukumar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa.
NCDC ta ce an gano nau'in cutar biyu ne ta hanyar amfani da fasahar gano tsarin kwayar halita ta 'genomic sequencing'.
Asali: Legit.ng