Bikin Kirsimeti: Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun hallaka mutane sun sace 33

Bikin Kirsimeti: Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun hallaka mutane sun sace 33

  • A ranar da mabiya addinin kirista ke bikin kirsimeti, wasu yan bindiga sun kai hari kauyuka 15 dake yankin Gusau a jihar Zamfara
  • Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa sun kashe mutane kuma sun sace mata 33, cikin su har da yan mata matasa
  • Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, amma tace sojoji sun kai ɗauki, kuma sun fatattaki maharan

Zamfara - Wasu yan bindiga sun kwashe awanni suna aikata ta'adi a kauyuka 15 dake yankin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda suka kashe mutum 7.

Mazauna yankunan da abun ya shafa sun bayyana cewa yan bindigan sun kaddamar da harin daga ranar Asabar (Ranar Kirsimeti) da yamma har zuwa safiyar Lahadi.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa yan bindigan sun yi awon gaba da aƙalla mutane 33 a harin.

Kara karanta wannan

Sabon Hari: Yan bindiga sun shiga gida-gida, sun yi awon gaba da jama'a a Zariya

Yan bindiga
Bikin Kirsimeti: Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun hallaka mutane sun sace 33 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kauyukan da yan bindigan suka kaiwa harin sun haɗa da; Geba, Kura, Duma, Gana, Tsakuwa, Gidan Kada da kuma Gidan Kaura.

Yan mutane suka ji da harin?

Premium Times ta rahoto mutumin na cewa mafi yawan mutanen ƙauyukan sun tsere da yammacin Lahadi saboda tsoron sake kawo hari.

Yace:

"Sun ɗauki mata 10 a ƙauyen Kura. Sannan a Bayauri, mun san sun sace mata 9, daga ciki har da yan mata, yayin da suka ɗauki mata bakwai a Gana. Daga nan suka zarce kauyen Duma suka ɗauki wasu bakwai."

Ya kuma kara da cewa mutanen da suka tsero daga harin da yan bindigan suka kai Kura, sun bayyana cewa an kashe mutum 7, amma ba su iya musu jana'iza ba.

Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da harin

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun ba kauyukan Zamfara wa’adi, sun ce a kawo N37m ko kowa ya dandana kudarsa

Kwamishinan yaɗa labaru na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya tabbatar da lamarin amma yace jami'an tsaro sun kai ɗauki tare da fatattakar maharan.

"Akwai sojoji dake kusa da kauyukan, kuma sun yi gaggawar ɗaukar matakai lokacin da aka kai hari Geba. Lokacin da sojojin suka isa yan bindigan sun jikkata mutane, amma sun fatattake su kuma suka kubutar da mutanen."

Mista Dosara ya musanta cewa babu wani mataki da jami'an tsaro suka ɗauka yayin hari a waɗan nan kauyuka 15.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai amsa waya ko sakon da aka tura masa ba.

A wani labarin na daban kuma mun tattara muku Muhimman abubuwa hudu da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Jagoran yan bindiga, wanda ake ganin ya addabi jihar Zamfara da wasu yankuna, Bello Turji, ya nemi a zauna zaman sulhu.

A ciki wasikar da ya aike wa shugaba Buhari , gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi, Turji ya nemi a cika wasu sharuɗɗa 4.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan bindiga sun sake ƙona mutum kurmus a cikin mota a jihar Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262