Rashin da'a ne ke sa likitoci suke tsundumawa yajin aiki, inji ministan Buhari
- Ministan Buhari ya bayyana yadda yake jin ba dadi idan likitoci suka shiga yajin aiki a Najeriya kasancewarsa likita
- Ya bayyana cewa, rashin da'a ne a ga likitoci na shiga yajin aiki kasancewar aikinsu shi ne kare rayukan alumma
- Hakazalika, ya bayyana yadda zuri'arsa ta kasance cike da likitoci tare da bayyana akidarsa ta kin jinin yajin aikin likitoci
Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce bai dace likitoci masu tsaron lafiyar al'umma su shiga yajin aikin ba kwata-kwata, Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja a wajen taron kaddamar da wasu dalibai shida da suka kammala karatun likitanci a Jami’ar Abuja a cikin Majalisar Likitocin lafiya da Hakora ta Najeriya.
Ya kuma bukaci sabbin daliban da suka kammala karatun likitanci da su gujewa akidar shiga yajin aikin da likitoci ke yi a kasar.
Ngige, a cewar wata sanarwar ta hannun mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar, Charles Akpan, ya bukaci daliban da suka kammala karatun likitanci da su kasance masu halin kirki da kuma kiyaye kyawawan dabi’u yayin gudanar da ayyukansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar TheCable ta rahoto ministan na cewa:
“Ni likita ne. Daya daga cikin ku da ake kaddamar a nan dana na biyu ne. Dana na farko shi ma likita ne. 'Yata ma likita ce.
“Ta hanyar da’a, rantsuwarmu a matsayinmu na likitoci ita ce ceton rayuka. Wannan shine babban aikinmu.
“Idan likitoci suka tafi yajin aiki, mutane suna mutuwa. Gaskiyar kenan. Rayuwar dan Adam ba ta da ma'auni. Ta yaya za ku dawo da mutanen da suka mutu sakamakon rashin zuwa wuraren aikin likitoci?
“Ba daidai ba ne likitoci su shiga yajin aikin. Na sha fadin haka sau da yawa a baya kuma zan ci gaba da fadi. Bai kamata likitoci su tafi yajin aikin ba. Don haka ya kamata ku daina yajin aiki domin amfanin bil’adama da kuma kyakkyawar sana’ar mu."
Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki
A wani rahoton, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, gwamnatin tarayya ta yabawa kungiyar likitoci mazauna Najeriya (NARD) saboda dakatar da yajin aikin da ta yi a fadin kasar wanda ya dauki tsawon kwanaki 63.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana haka lokacin da ya karbi shugabancin kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), wanda ya jagoranci mambobin zartarwa na NARD, a ziyarar da suka kai ofishinsa ranar Laraba a Abuja.
Ngige, wanda ya yabawa sabon shugabancin NARD wanda Dr Godiya Ishaya ke jagoranta, saboda rokon membobinta da su koma bakin aiki.
Asali: Legit.ng